Mutanen kasar waje ba za su samu damar kai ziyara ko zama a Sin ba
- Har masu rike da biza ba za su iya shigar kasar Sin daga Najeriya ba
- Gwamnatin Sin ta ce ta dauki wannan mataki ne saboda COVID-19
- Wannan dokar ba za ta yi tasiri a kan manyan jami’an gwamnati ba
Hukumomin kasar Sin sun ce sun takaita zirga-zirgar mutanen Najeriya da sauran kasashen ketare da ke rike da takardun bizan shiga kasar.
Jaridar Daily Trust ta ce haka zalika an hana masu takardun iznin zama yawo a kasar Asiyar.
A wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar Sin ta yi a ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamba, 2020, sun ce dakatarwar na wani lokaci ne.
KU KARANTA: Buhari ya zauna da Sultan, Sarkin Kano da Tawagar Sarakuna
Gwamnatin Sin ta ce ta dauki wannan mataki ne a dalilin annobar COVID-19 da ake fama da ita.
Ko da an shigo da wannan doka maras tsawon rai, sabon tsarin na hukumomin kasar ba zai yi aiki a kan manyan mutane da jami’an gwamnati ba.
Jakadancin kasar Sin ta kuma ce ba za ta rika bada takardar shaidar lafiya ga mutanen da ba ainihin ‘yan kasar ta ba daga yanzu zuwa wani lokaci.
KU KARANTA: Tafiya da Matasa zai taimaki Najeriya inji Ministar Tarayya
“Saboda sha’anin annobar COVID-19, Sin ta dauki matakin dakatar da shigowar wadanda ba ‘Yan Sin ba da ke Najeriya dauke da biza ko katin zama.”
“Masu shigowa Sin domin wata bukatar gaggawa za su iya neman biza a jakadancin kasar."
Wannan bai shafi bakin da su ka shigo Sin daga Najeriya bayan ranar 3 ga watan Nuwamba ba.
Za ku ji halin da mutanen Najeriya da kasashen Afrika za su shiga bayan Trump ya bar kujerar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng