Abia: ‘Dan Sanda Ya Bindige Abokin Aikinsa Bayan Rikici Ya Hada su

Abia: ‘Dan Sanda Ya Bindige Abokin Aikinsa Bayan Rikici Ya Hada su

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Abia tayi nasarar yin cafke wani ‘dan sanda da ya bindige abokin aikinsa bayan karamin hargitsi ya hada su
  • Ana gano yadda ‘yan sandan biyu suke aiki karkashin Ginger Onwusibe dake wakiltar kudancin yankin Ngwa a majalisar jihar
  • Kamar yadda kakakin ‘yan sandan ya sanar ranar Litinin, mummunan lamarin ya auku ne ranar Lahadi bayan wata ‘yar muhawara data shiga tsakaninsu

Abia - Rundunar ‘yan sandan jihar Abia ta bayyana yadda ta damko wani ‘dan sanda da ake zargi da bindige abokin aikinsa har lahira.

Abia Police
Abia: ‘Dan Sanda Ya Bindige Abokin Aikinsa Bayan Rikici Ya Hada su. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Marigayin, mai suna Samuel Ugor, mai mukamin sifetan l ‘yan sanda, ya rasa ransa ne sakamakon wata yar hatsaniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

‘Yan Ta’addan ISWAP sun Kai Harin Tsakar Dare Kan Sojoji, Sun Sha Luguden Wuta

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayyana, ‘yan sandan na aiki ne karkashin Ginger Onwusibe, ‘dan majalisa mai wakiltar kudancin mazabar Isiala Ngwa a majalisar jihar Abia.

Kakakin ‘yan sandan ya ce lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, inda ya kara da cewa ana kan bincike.

Jaridar TheCable ta rahoto cewa, Ogbonna ya siffanta lamarin a matsayin abin takaici kuma abin kushewa, inda ya kara da cewa:

”’Yan sandan na aiki ne a SPU Base 15 na Anambra, amma suna karkashin ‘dan majalisa ne”.

Duk da ba a cika samun aukuwar irin wannan lamarin ba, hakan ya sha faruwa a baya, ‘yan sanda na harbin abokan aikinsu saboda dalilai daban-daban.

Wata sabuwa: Jami'in dan sanda ya harbe abokin aikinsa dan sanda a jihar Kano

A wani labari na daban, An harbe wani jami’in dan sanda mai suna Sufeto Ya’u Yakubu a hedkwatar ‘yan sanda na yankin Warawa da ke jihar Kano, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An Bindige Mutum 1, Wasu 18 Sun Jigata a Arangamar ‘Yan Daban PDP da APC a Zamfara

An ce Sajan Basharu Alhassan ne, wani abokin aikinsa a sashen da suke ya harbe shi.

Yayin tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an garzaya da marigayin zuwa babban asibitin Wudil inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Kiyawa ya kara da cewa nan take aka cafke Sajan Basharu Alhassan.

Ya kara da cewa yanzu haka an tura wanda ya yi kisan zuwa CID na jihar, za a yi masa gwaji don tabbatar da lafiyar kwakwalwarsa kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sama’ila Dikko ya ba da umarni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel