Ba ma rabon N45,000 a matsayin tallafin korona, in ji hukumar NCDC

Ba ma rabon N45,000 a matsayin tallafin korona, in ji hukumar NCDC

- Hukumar NCDC ta ce bata kowani shiri na bayar N45,000 a matsayin tallafi

- A cewar hukumar lafiyar, sakon da ke ya yawo yana sanar da batun biyar tallafin a matsayin karya

- Hukumar lafiyar ta gargadi ‘yan Najeriya da su tabbatar da sahihancin labari kafin su yada shi

Wani rahoto daga jaridar Daily Trust tare da hadin gwiwar Africa Check ya nuna cewa cibiyar kula da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) bata rabon N45,000 a matsayin tallafin COVID-19.

Wallafar jaridar ya yi watsi da jerin sakonni da ake yadawa a WhatsApp wanda ke ikirarin cewa hukumar lafiyar na bayar da N45,000 saboda annobar da ya fitini kasar.

“Ka yi nasarar samun N45,000 daga NCDC saboda annobar coronavirus a Najeriya kira mu ta lambar 09063756881 domin karban kudin,” kamar yadda sakon yake.

An tattaro cewa babu wata sanarwa daga hukumar lafiyar wanda ke tabbatar da sakon da ake magana a kai.

Tawagar labarai ta NCDC da suke magana ga Africa Check sun yi bayanin cewa sakonnin ba gaskiya bane.

Ba ma rabon N45,000 a matsayin tallafin korona, in ji hukumar NCDC
Ba ma rabon N45,000 a matsayin tallafin korona, in ji hukumar NCDC
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi sabbin nade-nade shida, ya ambaci Kangiwa a matsayin shugaban PWDC

“Duk wani sako kan kudin tallafi daga hukumar NCDC karya ne. Dan Allah ku dauki alhaki sannan ku tabbatar da dukkanin bayanai kafin ku yada shi,” in ji NCDC.

Tuni hukumar lafiyar ta fara aika sakon gargadi ga ‘yan Najeriya game da sakonnin WhatsApp ta shafukan zumunta da sakon waya.

Idan za a tuna kimanin watanni hudu da suka gabata, kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya karyata wani rahoton cewa shi ya ce ‘yan Najeriya masu BVN za su samu N30,000 a matsayin kudin tallafi.

A cewarsa, rahoton wanda ya yi fice a shafukan sadarwa duk karya ce. Ya karyata hakan a wani wallafa da ya yi a shafin twitter a ranar Asabar, 28 ga watan Maris.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da labarin.

A wani labarin kuma, Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 321 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:45 na daren ranar Litinin 24 ga Agustan shekarar 2020.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel