Ragon maza: 'Ina yawan shan duka a wurin mata ta' - Miji mai neman saki

Ragon maza: 'Ina yawan shan duka a wurin mata ta' - Miji mai neman saki

Wani dan kasuwa mai suna Gbade Olaniyi ya shigar da karar matarsa, Olubunmi, a gaban wata kotun gargajiya da ke Ile-Tuntun a garin Ibadan domin neman a raba aurensu saboda dukan da ya ke yawan sha a hannunta.

Da ya ke bayar da shaida a gaban kotu, Olaniyi ya bayyana cewa; "mata ta tafi karfina. Ta rabani da abokaina da 'yan uwana.

"Duk lokacin da wani karamin sabani ya shiga tsakanimu sai ta zabgeni da mari. Ko a ranar 2 ga watan Agusta, kimanin kwanaki goma da suka gabata, sai da ta mareni, ta yi min rauni da farcen hannunta.

"Ta ce tana yi min hakan ne saboda ba na fada mata daga inda nake duk lokacin da ta tambayeni idan na dawo gida.

"Ta wulakanta aure ta hanyar wofantar da nauyin da ke wuyanta. Ta kan bar gida, ta yi kwanaki ko watanni, ba tare da na san inda take ba, ba kuma tare da wani dalili ba," a cewarsa.

Matar ta amince da bukatar mijin ta neman a raba aurensu.

Ragon maza: 'Ina yawan shan duka a wurin mata ta' - Miji mai neman saki
Ragon maza: 'Ina yawan shan duka a wurin mata ta' - Miji mai neman saki
Asali: Twitter

"Mai girma mai shari'a, mijina ya zama fakiri, yaranmu ko suturar kirki basu da ita.

"Wasu lokutan na kan bar gidansa saboda ya gaza daukan nauyina, hatta a lokutan da na ke da juna biyu.

"Na mareshi ne saboda na samu labarin yana lalata da wata karamar kwaila da ke zaune kusa da gidanmu.

DUBA WANNAN: 'Dukkan Musulman Najeriya sun aikata laifin batanci': Sakon Shekau a kan hukuncin kashe mawaki a Kano

"Na samu labarin yana aikata hakan ne saboda 'yar uwar yarinyar ta zo har gida domin yi masa gargadi. Sannan ina da shaidar sakon katin waya da na soyayya da ya ke aika mata. Har Otal su ke tafiya tare," kamar yadda Olubunmi ta shaidawa kotu.

Alkalin kotun, Cif Henry Agbaje, ya bayyana cewa ma'auratan sun gaza gabatar da gamsassun hujjoji, a saboda haka akwai bukatar su kara gabatar da shaidunsu da karin hujjoji.

Ya bukaci kowannensu ya zo da magabatansa a zaman kotun na gaba da za a yi domin yanke yanke hukunci a ranar 19 ga watan Agusta.

NAN

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel