Yanzu Yanzu: Lawan ya yi wa Kalu maraba da dawowa majalisar dattawa

Yanzu Yanzu: Lawan ya yi wa Kalu maraba da dawowa majalisar dattawa

- A karshe Sanata Orji Kalu ya koma majalisar dattawa yan kwanaki bayan sakinsa daga gidan yari na Kuje

- An tattaro cewa Kalu ya samu tarban maraba da dawowa daga shugaban majalisar dattawa Lawan a ranar Talata, 9 ga watan Yuni

- An yanke wa Sanata Kalu shekaru 12 a gidan yari kan zargin satar naira biliyan 7.65 amma sai daga bisani kotun koli ta soke hukuncin

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a ranar Talata, 9 ga watan Yuni, ya yi wa bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu maraba da dawowa majalisar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kwanan nan ne aka saki Sanata Kalu daga wani gidan gyaran halayya na Najeriya.

Da farko, Legit.ng ta rahoto cewa Lawan, a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni, ya jagoranci sauran sanatoi inda suka ziyarci Sanata Kalu a gidansa.

Yanzu Yanzu: Lawan ya yi wa Kalu maraba da dawowa majalisar dattawa
Yanzu Yanzu: Lawan ya yi wa Kalu maraba da dawowa majalisar dattawa Hoto: President of the Senate
Asali: Facebook

Manyan yan majalisar dokokin sun ziyarci Kalu, bulaliyar majalisar dattawa, biyo bayan sakinsa da aka yi daga gidan yari a ranar Laraba, 3 ga watan Yuni.

KU KARANTA KUMA: Edo: Kofofinmu a bude suke ga fusatattun mambobin APC - PDP

An saki tsohon gwamnan na jihar Abia bayan ya shafe watanni a gidan gyaran hali na Kuje.

An hukunta Kalu a watan Disamban 2019 kan zargin satar kudi naira biliyan 7.65 mallakar jihar Abia. Sai dai kuma kotun koli ta soke hukunin yayinda aka yi umurnin sake shari’a.

Idan za ku tuna, a baya mun kawo maku cewa masu zanga-zanga a karkashin kungiyar Concerned Citizens of Abia North daga jihar Abia a ranar Talata, sun mamaye majalisar dokokin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Sun yi kira ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan da ya yi gaggawan sanya kujerar bulaliyar masu rinjaye a majalisar, Sanata Orji Uzor Kalu a kasuwa.

Kalu ya kasance dan jam’iyyar All Progressives Congress kuma sanata mai wakiltan yankin Abia ta arewa.

A cewar kungiyar, kaddamar da kujerar a kasuwa zai sa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta gudanar da sabon zabe na wanda zai wakilci Abia ta arewa a majalisar dattawan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel