Sulhu da 'yan bindiga: Masari ya bayyana wadanda su ka ci amanar gwamnatinsa

Sulhu da 'yan bindiga: Masari ya bayyana wadanda su ka ci amanar gwamnatinsa

- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce 'yan bindigar da basu rungumi tsarin sulhu ba sun cigaba da kai hare - hare

- Masari ya ce ba zai kara yin sulhu da 'yan bindiga ba saboda cin amanar da barayin daji su ka yi wa gwamnatinsa

- Ya ce yanzu lokaci ne da ya kamata jami'an tsaro su gwada yin sulhu da 'yan bindiga

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce ba zai kara yin sulhu da 'yan bindiga ba saboda cin amanar da aka yi wa gwamnatinsa.

A cewar gwamnan, barayin da ke fashi a dazuka sun ci amanar yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla da su.

Yayin hirarsa da sashen Hausa na BBC, Masari ya ce daga cikin 'yan bindigar da ke kai hare - hare a jihar Katsina akwai wadanda su ka fito daga jihar Kaduna da Zamfara da 'yan Nijar.

Masari ya bayyana cewa gwamnatinsa ce ta fara zuwa da tsarin yin sulhu da 'yan bindiga a shekarar 2016.

Gwamna Masari ya ce da farko sulhun ya yi tasiri wajen dawo da zaman lafiya a jihar Katsina kafin daga bisani 'yan bindigar su ci amanar gwamnati.

Sulhu da 'yan bindiga: Masari ya bayyana wadanda su ka ci amanar gwamnatinsa
Aminu Bello Masari
Asali: Twitter

A cewar Masari, 'yan bindigar da ba su rungumi sulhun ba ne suka zagaye suke kai hare - hare.

Masari ya ce jami'an tsaro ne ya kamata su gwada yin sulhu da barayin a wannan karon, don shi kam ba zai kara yin sulhu da 'yan bindigar ba.

"Zaman lafiya ya gagara samuwa duk da mun bi hanyar sulhu da maslaha, mun yi iya bakin kokarinmu a matakin gwamnatin jiha," a cewar Masari.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi magana a kan kisan matashiya a cikin Coci

Ya kara da cewa gwamnati ta cika alkawuran da ta dauka a yarjejeniyar da aka kulla; ta soke 'yan sa kai, ta budewa makiyaya hanyoyin bi da shanunsu da kuma samar mu su hanyoyin da za su kawo kayansu kasuwanni.

Masari ya kara da cewa kukan da gwamnatin jihar ta yi ne ya sa gwamnatin tarayya ta turo dakarun soji da jiragen yaki da za su ke sintiri a tsakanin Katsina, Sokoto da Zamfara domin kawo karshen aiyukan 'yan bindiga.

Amma ya ce jami'an tsaron na kukan rashin kayan aiki. "Ba su da wadatattun kayan aiki, suna bukatar kayan aiki sosai," in ji Masari.

"Babu wadatattun kayan aiki a wurin jami'an tsaro, su na bukatar kayan aiki na kirki," a cewar Masari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel