Ana tsaka da billowar coronavirus: Jami’an gwamnatin Yobe sama da 20 sun tafi Dubai

Ana tsaka da billowar coronavirus: Jami’an gwamnatin Yobe sama da 20 sun tafi Dubai

Rahotanni sun kawo cewa jami’an gwamnatin jahar Yobe sama da guda ashirin ne suka tafi tarayyar Turai a makon da ya gabata yayinda ake tsaka da barkewa annobar coronavirus.

Tafiya kasar wajen da suka yi ya haifar da tsoro a jahar yayinda mazauna Damaturu suka yi kira ga a killace su a Lagas ko Abuja kafin sui so Damaturu da sauran yankunan jahar.

Wasu mutane da suka zanta da manema labarai a Damaturu sun nuna damuwa kan dalilin da ya sa jami’an za su tafi waje a daidai wannan lokacin da kowa ke kokarin rage shigowa da yada cutar coronavirus a kasar.

Ana tsaka da billowar coronavirus: Jami’an gwamnatin Yobe sama da 20 sun tafi Dubai

Ana tsaka da billowar coronavirus: Jami’an gwamnatin Yobe sama da 20 sun tafi Dubai
Source: UGC

Mafi akasarin mutanen da suka yi magana kan zargin boye sunansu sun yi kira ga killace jami’an da zaran sun dawo kafin su shigo Damaturu domin tsoron kwasar cutar.

Sai dai kuma kwamishinan lafiya a jahar Yobe, Dr. Mohammed Lawan Gana ya ce tawagarsa na agajin gaggawa kan coronavirus na tuntubar dukkanin jami’an inda suke sanar dasu abunda za su yi da wanda za su guji yi domin daukar matakin hana daukar cutar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa sama da jami’an gwamnatin jahar Yobe ashirin ciki harda wasu kwamishinoni, hadimai, da mambobin majalisar dookin jahar, sakatarorin dindindin, daraktoci a ma’aikatun gwamnatin jahar ne suka tafi kasar Dubai domin halartan taron horarwa na kasa da kasa.

A cewar kwamishinan, za a tafiyar da jami’an Kaman kowani matafiyi da ya shigo kasar bisa ga shawarar gwamnatin tarayya kan matafiya.

KU KARANTA KUMA: Abinda yasa har yanzu Buhari bai yi jawabi a kan Coronavirus ba - Lai Mohammed

A wani labarin kuma mun ji cewa, Majalisar wakilai ta ce bata tunanin dakatar da zamanta a tsaka da barkewa annobar coronavirus.

Benjamin Kalu, mai magana da yawun majalisar wakilan, ya bayyana haka a yayinda ya ke jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 19 ga watan Maris.

Akwai yan majalisa 360 a majalisar wakilan kasar da kuma dubban baki da ake samu duk mako.

Domin hana yaduwar annobar, tuni dai wasu gwamnatocin jihohi suka hana taron da ya fi naa mutane 50.

Kalu ya ce yan majalisan za su ci gaba da zamansu domin samun damar sassaita zafafan batutuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel