Najeriya za ta rasa makudan miliyoyin Daloli idan Nijar ta ja wutan kanta

Najeriya za ta rasa makudan miliyoyin Daloli idan Nijar ta ja wutan kanta

Najeriya za ta rasa wasu kudin shiga da ta ke samu daga makwabta Jamhuriyyar Nijar. Gwamnatin Najeriya na iya daina samun kudin lantarkin da ta saba samu daga kasar.

Da zarar Nijar ta jawo wutan lantarkinta da kanta, Najeriya za ta daina samun kudi daga hannunsu. Wani Masani a kan harkar wuta ne ya fara jan kunnen gwamnatin Najeriya.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa bayan kasar Nijar, Najeriya ta na fita da wutar lantarki zuwa sauran kasashen Afrika na-kusa da su ka hada da Togo, Chad da kuma kasar Benin.

Najeriya ta kan ba wadannan kasashe megawatts 350 zuwa 400 duk shekara. A dalilin wannan yarjejeniya, gwamnatin Najeriya ta kan samu Dala miliyan 582 zuwa miliyan 665.

KU KARANTA: Gwamnati ta ce za ta kara kudin wutar lantarki a Najeriya

Najeriya za ta rasa makudan miliyoyin Daloli idan Nijar ta ja wutan kanta
Kasar Najeriya ta na ba Nijar da wasu kasashe wutar lantarki
Asali: Facebook

Mohammed Eti, wanda Darekta ne a wani kamfanin wuta, ya bayyana cewa da zarar Najeriya ta kyale Nijar ta haki Kogin Neja ta dabin Fouta Djullion, Najeriyar ta shiga cikin matsala.

Eti ya ke cewa idan har Jamhuriyyar Nijar ta cin ma wannan dama, to Najeriya ba za ta iya fitar da lantarki zuwa kasar Yammacin Afrikan ba, wannan zai kuma rage mata kudin shiga.

Wannan Masani ya ce Najeriyar da ke ba wadannan kasashe wuta, ta na zaune ne a cikin duhu. Gwamnatin Najeriya ta kan saida lantarkin ne ga kasashen a farashin ‘yan kasuwa.

Najeriya ta na ta fama da megawatt 5000 duk da makudan kudin da gwamnatin tarayya ta batar domin ganin an inganta sha’anin wutar lantarki. Har yanzu ba a iya kai wa ga ci ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel