Hisbah ta kama wasu matasa 26 da suka yi shigar mata a wurin biki a Kano

Hisbah ta kama wasu matasa 26 da suka yi shigar mata a wurin biki a Kano

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta sanar da cewa ta kama wasu maza 26 da suka yi shigar mata a wurin wani bikin taya murnar ranar zagayowar haihuwa.

Mataimakin kwamandan rundunar Hisba, Tasiu Ishaq, ya ce sun tsare matasan, da suka yi shigar mata, ranar Lahadi.

"Ba kankanin abin kunya bane a ce maza lafiyayyu zasu ke halayya irin ta mata," a cewarsa.

Kwamanda Ishaq ya ce sun yi wa matasan wa'azi a kan illar laifin da suka aikata tare da tilasta su yin Sallah kafin su mika su ga iyayensu.

Daya daga cikin matasan da aka kama ya shaida wa BBC cewa abokinsa ne ya gayyace shi zuwa wurin bikin tare da bayyana cewa wanda ya shirya bikin ya tsere yayin da dakarun Hisbah suka dira tare da daka wasoso a kan jama'ar da ke wurin.

Hisbah ta kama wasu matasa 26 da suka yi shigar mata a wurin biki a Kano
Dakarun Hisbah
Asali: UGC

"Sun yi mana wa,azi kuma sun saka mu yin Sallah yayin da muke hannunsu. Nayi nadamar abinda ya faru kuma da yardar Allah zan canja hali," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Buhari bai nada jarumi Nura Hussain a matsayin kwamishina ba a NAHCOM

Kano na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da suka kaddamar da shari'ar Musulunci tun a shekarar 2001.

Dakarun Hisbah suna da ikon kama mutanen da suka aikata abin da ya saba da dokokin addinin Islama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel