Bidiyo: Yadda wata mata ta yiwa mijinta dukan tsiya saboda ya kirata da karuwa a bainar jama'a

Bidiyo: Yadda wata mata ta yiwa mijinta dukan tsiya saboda ya kirata da karuwa a bainar jama'a

- Wani bidiyon mata na jibgar mijinta ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani

- Matar ta zargi mijin da zaginta a yayin da musu ya hadasu a motar haya

- Ta turmushe mijin tana jibga amma sai yayi biris da ita, lamarin da yasa wadanda ke motar suka dinga bata hakuri

Wani bidiyo mai cike da abun mamaki da al'ajabi ya yawaita a kafafen sada zumuntar zamani. A bidiyon, an ga wata mata ne tana jibgar mijinta kamar Allah ya aikota. A cewar matar, mijin ne ya zageta, lamarin da ya bata mata rai har ta dinga dukanshi.

An gano cewa, ma'auratan sun hau motar haya ne kuma sai kwatsam suka fara wani musu. Hakan yasa mijin ya dubi matar tare da kiranta da karuwa.

Maida martanin wannan zagin ne yasa matar ta dinga dukan mijin kamar an aikota.

A yayin da ta turmushe mijin tana duka, ya yi biris da ita kamar bai san tana yi ba. Tuni sauran fasinjoji suka dinga bata hakuri don samun zuciyar matar ta lafa.

KU KARANTA: Tirkashi: Wata mata ta kashe danta na cikinta saboda ya koma dan luwadi

Wata budurwa ce ta dau bidiyon, kuma ta watsa a kafafen sada zumuntar zamani.

Wannan dai ya zamo sabon al'amari a ko ina. Saboda maza ne aka sani da fushi tare da jibgar matansu matukar wani abu ya hadasu.

Amma a wannan lamarin, komai ya sha banban. Don kuwa matar ce mai karfin halin dukan mijin, duk da kuwa a motar haya suke ba a cikin gidansu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel