Ku kasance masu gaskiya da wayewa - Ganduje ga sabbin kwamishinoni

Ku kasance masu gaskiya da wayewa - Ganduje ga sabbin kwamishinoni

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci sabbin kwamishinonin da aka rantsar da su gudanar da ma’aikatunsu cikin wayewa, tare da kudirin kai jihar zuwa ga matakin cigaba.

Da yake magana a taron rantsar da sabbin kwamishinonin guda 20, Ganduje ya bukace su da su kasance masu sa idanu, fasaha, gaskiya da kuma jajircewa wajen gudanar da ma’aikatunsu mabanbanta.

Ganduje ya ce: “Mutanen Kano suna fatan samun cigaba daga gare ku, muna sanya ran za ku kasance masu gaskiya, fasaha da jajircewa akan hakkokin da suka rataya a wuyanku. Kuma muna sanya ran za ku yi iya bakin kokarinku domin kai Kano zuwa mataki na gaba.

“Ku kasance tsararru sosai, masu fasaha domin ku bayar da gudunmawarku wajen cigaban tattalin arzikin Kano. Ana sanya ran za ku yi aiki a matsayin tawaga tare da sakatarorin dindindin da daraktoci domin aiwatar da manufofinmu da kyau. Ana sanya ran za ku mutunta kujerunku da kuma aiki kai da fata tare da jama’a.

Kwamishinonin da aka rantsar sun hada da kwamishinan watsa labaru Muhammad Garba, kwamishinan kananan hukumomi Muratala Sule-Garo, Musa Iliyasu Kwankwaso, Ibrahim Mukhtar, Kabiru Ibrahim Getso, Shehu Na-Allah Kura, Mukhtar Ishaq da Muhammad Tahir Adam.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Shugaba Buhari ya fatattaki hadimai 35 a ofishin Osinbajo

Sauran sun hada da Ma’azu Magaji, Nura Muhammad-Dankade, Zahra’u Umar-Muhammad, Aminu Ibrahim-Tsanyawa, Sadiq Aminu-Wali, Muhammad Baffa-Takai da Kabiru Ado-Lakwaya, Mariya Mahmoud-Bunkure, Ibrahim Ahmad-Karaye, Mahmoud Muhammad-Dansantsi, Muhammad Sanusi-Sa’id da Lawan Abdullahi-Musa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel