Yanzun nan: Sojoji sun kashe yan bindiga 39 a Zamfara

Yanzun nan: Sojoji sun kashe yan bindiga 39 a Zamfara

Dakarun sojoji sun kashe akalla yan bindiga 39 a wasu ayyuka mabanbanta guda biuyu da suka gudanar a Zamfara cikin wannan makon, kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito.

Kyaftin Oni Oisan, kakakin shirin Operation Hadarin Daji, wanda ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Asabar, yace an gudanar da ayyukan ne a yankunan Bakura da Anka da ke jihar.

A cewarsa, an kashe 19 daga yan bindigan a wani arangama da sojoji a jejinan Anka yayinda aka kashe 20 a Bakura.

Orisan ya jaddada cewa sojojin ba za su farma kowani tubabben dan bindiga ba.

Sai dai kuma ya bayyana cewa za a lallasa wadanda ba tubabbu ba dake dauka bindigogi suna yawo a dadi mai yawa.

Ya shawarci wadanda ba tubabbu ba da su mika makamansu ga hukumomin da ya kamata sannan su rungumi shirin zaman lafiya na gwamnatin jihar.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun kama manyan kwamandojin Boko Haram 10 (kalli jerin sunayensu)

NAN ta ruwaito cewa tun daga fara shirin zaman lafiya da sulhu kimanin watanni biyar da suka gabata, zaman lafiya ya dawo garuruwa da dama.

Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai ya ziyarci jihar kwanan nan, ida yayi alkawarin cewa sojoji za su cigaba da aiki domin dorewa zaman lafiya a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel