Najeriya ce kasa ta uku da 'yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka - Rahoton masana

Najeriya ce kasa ta uku da 'yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka - Rahoton masana

Cif Edinen Usoroh, shugaban kungiyar cibiyoyin tsaro masu lasisi a Najeriya (ALPSPN) reshen jihar Filato, ya ce yanzu haka Najeriya na kan mataki na uku a cikin jerin kasashen duniya da aiyukan ta'addanci suka kazanta.

Usoroh ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin da yake gabatar da jawabi a wurin wani taro na kwana daya da aka shirya domin wayar da kai a kan aiyukan ta'addanci.

Ya ce alkaluman da kungiyar duniya mai sa ido a kan harkokin ta'addanci ta fitar a shekarar 2018 ne ya nuna hakan.

"Har yanzu Najeriya na mataki na uku a cikin jerin kasashen duniya da aiyukan ta'addanci suka yi wa katutu, kamar yadda rahoton kungiyar sa ido a kan aiyukan ta'addanci na shekarar 2018 ya nuna.

"Kasashen duniya biyar da aiyukan 'yan ta'adda suka kazanta sune; Iran, Afghanistan, Najeriya, Syria da Pakistan.

"Boko Haram ce babbar kungiyar 'yan ta'adda a Najeriya da ma wasu kasashen Afrika da ke yankin Sahara," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Jerin al'mura 5 da Buhari ya amince da su domin murnar cika shekaru 59 da samun 'yancin Najeriya

Usoroh, wanda shine shugaban kamfanin tsaro na 'Guards Ltd', ya ce jami'an tsaron Najeriya sun kasa magance matsalar Boko Haram ne saboda a cikinsu akwai batagari.

A cewarsa, barazanar cikin gida da rundunar sojoji ke fuskanta, ita ce ta hana samun nasara a yakin da suke yi da 'yan Boko Haram.

"Daga lokacin da dan ta'adda ya samu 'yan leken asiri a cikin rundunar tsaro, ita kanta rundunar tsaron ta shiga cikin hatsari," a cewarsa.

Usoroh ya kara da cewa bayan aiyukan ta'addanci, Najeriya na fama da matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane, fyade, kisan jama'a don yin tsafi, rikicin makiyaya da manoma, hare-haren 'yan bindiga da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel