Sulhu alheri ne: Masu garkuwa da mutane sun sako kananan yara guda 10 a Katsina

Sulhu alheri ne: Masu garkuwa da mutane sun sako kananan yara guda 10 a Katsina

A cigaba da ribatar tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin jahar Katsina da kungiyoyin yan bindiga masu garkuwa da mutane a jahar, yan bindigan sun sake sako wasu kananan yara guda 10, inji rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun sako yaran ne a ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, wanda dama sun sace yaran ne daga kauyen Ruma, na karamar hukumar Batsari ta jahar Katsina.

KU KARANTA: Buhari zai kammala gyarar wutar Najeriya kafin karshen mulkinsa – Minista

Yaran sun ce kwanansu 32 a hannun yan bindigan kafin wannan lokaci da aka sakesu, inda suka ce ana basu abinci a kullum, kuma babu wani dan bindiga daya ci zarafinsu ko kuma ya nemi ya yi musu fyade.

Tuni dai aka mika wadannan yara ga shugaban riko na karamar hukumar Batsari, wanda zai tattarasu ya kai su zuwa asibiti domin a duba lafiyarsu kafin ya a mikasu ga iyayensu da danginsu. Zuwa yanzu dai gwamnatin jahar ta yi sanadiyyar sako mutane 67 daga hannun yan bindiga a Katsina.

A wani labarin kuma, yan bindiga sun sako mutane 30 da suka yi garkuwa dasu a ranar Lahadi, 15 ga watan Satumba, inda aka mikasu ga gwamnan Katsina a fadar gwamnatin jahar Katsina.

An dauke mutanen ne daga kauyukan Kankara da Shimfida, duk a cikin karamar hukumar Jibia, daga nan yan bindigan suka tafi dasu mafakarsu dake dajin Dansadau a jahar Zamfara.

Wata daga cikin wadanda aka sako, Zinatu Sani ta bayyana cewa ita da yaranta biyu yan bindigan suka dauke har gida, kuma suka nemi kudin fansa miliyan 20, daga bisani suka rage zuwa miliyan 6, amma duk da haka an kasa biya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel