Tirkashi: Daga cewa na rufe idona zai bani kyauta, ban yi aune ba sai jin wuka nayi a makogwaro na - Matar da mijinta yayi yunkurin yankata

Tirkashi: Daga cewa na rufe idona zai bani kyauta, ban yi aune ba sai jin wuka nayi a makogwaro na - Matar da mijinta yayi yunkurin yankata

- Kotu ta zargi wani mutumi mai suna Shaun May da yunkurin yin kisan kai, bayan yayi kokarin kashe matarsa

- May dai ya bukaci matarsa mai suna Laura da ta rufe idonta zai bata kyauta mai kyau, kawai sai ji tayi yana kokarin yi mata yankan rago

- Ta ce suna tare da mijinta na tsawon shekaru masu yawa kuma basu taba samun matsala ba, amma ba ta san yadda aka yi yake kokarin yi mata yankan rago ba

Wani mutumi wanda ya nemi matar shi da ta rufe idon ta zai bata kyauta mai ban mamaki, ya nemi yayi mata yankan rago, amma hakar shi ba ta cimma ruwa ba, inda aka kama shi da laifin kisan kai.

Mutumin mai suna Shaun May ya nemi matar tasa ta rufe idonta, inda ya fara kirgawa daga goma, matar tasa mai suna Laura ba tayi aune ba sai jin wuka tayi a makogwaronta, hakan ya biyo bayan korarsa aiki da aka yi a watan Oktoba dinnan da ya gabata.

Shaun mai shekaru 34 an kama shi da laifin kokarin aikata kisan kai bayan ya nemi ya yankata a lokacin da ya nemi ta kwanta akan gado ta rufe idonta.

Laura ta bayyana cewa tana tare da mijin nata na tsawon shekaru shida kuma suna son junansu kwarai da gaske. Ta ce da wuya wani abu ya hada su wanda har zai sanya aji kansu.

KU KARANTA: Tashin hankali: Kudan zuma sun kai wa wani dan majalisar APC hari har gida, kwanaki uku da samun nasarar shi a kotu

A wannan watan Oktoban da ya gabata ma'auratan sun dawo daga kasar Korea yawon bude ido, bayan shigowar su gida May ya ce mata zai sauka kasa kamar yaji motsi.

Bayan ya dawo yake ce mata ya kawo mata wata kyauta mai ban mamaki, sai yace mata ta rufe idonta idan tana so, ta kuwa rufe idonta, sai ya fara kirgawa daga goma.

"Ban yi aune ba sai ji nayi an danne mini kafada ta yana kokarin yanka ni, sai na fara ihu, na samu na ture shi da kyar, sai na ganshi da wukake guda biyu a hannu, yana ce mini shi fa kashe kanshi zai yi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel