Wasu Iyaye su na saida ‘Ya ‘yan su saboda samun abin Duniya a Najeriya

Wasu Iyaye su na saida ‘Ya ‘yan su saboda samun abin Duniya a Najeriya

Jaridar Daily Trust ta kawo wani dogon rahoto mai ban takaici a game da yadda wasu Iyaye da su ka saida ‘Ya ‘yan su da sunan su na neman kudin sayan wayar zamani ko kuma su samu kudi.

A wannan rahoto da Jaridar ta yi an samu wasu Iyaye akalla 15 da su ka saida Yaran na su daga Watan Fubrairu zuwa Watan Yunin bana. A haka wannan Iyaye su ka tara kudi Naira miliyan 5.4.

Daga cikin wadannan Iyaye akwai wata Mata mai ‘ya ‘ya 2 mai suna Miracle Omovuokpor a jihar Edo da ta fadawa ‘yan sanda cewa ta saida jaririnta mai wata 6 a Duniya a kan kudi N200, 000.

Omovuokpor ta ce takaici ta sa ta saida Yaron ta a Yulin 2018 bayan da takaicin talauci ya ishe ta. Wannan mata ta ce da haka ta tarawa Mijinta kudin da ya fara kasuwanci domin ciyar da Iyali.

KU KARANTA: Hayan gida a Abuja ya sa ‘Yan Majalisar sun bazama neman aron kudi a banki

Ita kuma Misis Nneka Donatus ta saida Jaririyar da ta haifa a kan kudi N600, 000. Donatus mai ‘ya ya 5 ta yi amfani da wannan kudi ne wajen sayan wayar zamani da atamfa da kuma takalma.

Akwai kuma Daniel Bassey da Mai dakinsa Magdalene a Kuros Riba, da su ka saida ‘Dan su mai shekaru biyu wajen masu sayen yara a cikin Garin Fatakwal domin su samu kudin biyan hayar gida.

A Agustan 2018 kuma ‘yan sanda su ka kama wani Kenneth Ofoke da ya saida Tagwayen jariransa a N500, 000. Kenneth Ofoke Mutumin Ebonyi ya saida yaran na sa ne domin ya biya kudin asibiti.

A Garin Afam da ke cikin karamar hukumar Oyigbon jihar Ribas, an kama wani Richard da Iyalinsa Chidinma Benson da laifin saida yaransu mai kwana daya a Duniya a bara a kan N250, 000.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel