'Yan sanda sun bankado wani kamfanin kera bindigu a kudancin Najeriya

'Yan sanda sun bankado wani kamfanin kera bindigu a kudancin Najeriya

Kwamishinan 'yan sanda a jihar Imo, Rabiu Ladodo, ya ce 'yan sanda sun kama wani mutum da ake kira Eze Ajoku, mai shekaru 63, a garin Agwa da ke karamar hukumar Oguta, wanda ya kware wajen kera bindigu.

Da ya ke bayyana hakan ranar Laraba, Ladodo ya ce mutumin na daga cikin mutane 22 da rundunar 'yan sanda ta kama, cikinsu har da jami'in dan sanda mai mukamin sufeta, bisa aikata laifukan da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

Daga makaman da ya lissafa cewar jami'an rundunar 'yan sanda sun samu a kamfanin kera bindun akwai karamar bindiga guda daya, carbin alburushi, manyan bindigu masu baki biyu guda biyu, babbar bindiga mai baki daya guda 8.

'Yan sanda sun bankado wani kamfanin kera bindigu a kudancin Najeriya

'Yan sanda sun bankado wani kamfanin kera bindigu a kudancin Najeriya
Source: Twitter

Ragowar sun hada injin wasu bindigu guda 9, carbin alburusai biyu, wani kwanson alburusai na musamman, wani inji (drilling machine) guda daya, zarton yanka karfe guda 9 da sauran su.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun yi awon gaba da wata mai jego

Ladodo ya kara da cewa an jami'in dan sanda, Salvation Kpun, mai mukamin sufeta, a wata unguwa dake gefen garin Oweri bisa zargin hannunsa a aikata fashi da makami.

Kwamishinan ya ce yanzu haka jami'an 'yan sanda na bin sahun wani jami'in soji da ke cikin tawagar 'yan fashin da Salvation ke jagoranta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel