A kebance kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa zuwa Arewa maso Yamma - Sanata Kabiru Gaya ya gargadi APC

A kebance kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa zuwa Arewa maso Yamma - Sanata Kabiru Gaya ya gargadi APC

Sanata Kabiru Gaya, ya gargadi jam'iyya mai ci ta APC da ta kebance kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa zuwa yankin Arewa maso Yamma domin ramawa kura kyakkyawar aniyya na kuri'un da ta samu a yankin yayin babban zabe.

Sanatan mai wakilcin shiyyar Kano ta Kudu a zauren majalisar dattawan kasar nan ya yi wannan furuci a ranar Laraba yayin ganawar sa da manema labarai cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Sanata Kabiru ya gargadi jam'iyyar APC akan kada ta kuskura ta yiwa al'ummar yankin Arewa maso Yamma butulci bayan samun kuri'u fiye da miliyan shida a yayin babban zaben kasa da aka gudanar watanni kadan da suka gabata.

A yayin da yake hankoron samun kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Kabiru Gaya ya ce duk da ba ya da wata alaka da kididdigar alkaluma na hasashe, ya fi dukkanin masu hakoron kujerar rinjaye na samun nasarar.

KARANTA KUMA: Mutane 17 sun raunata yayin da mota ta tumurmusa masu Sallar Idi a kasar Indiya

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, sauran masu matsin lamba ta hankoron kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa a sabuwar majalisar ta tara a tarihin dimokuradiyyar kasar nan sun hadar da Sanata Orji Kalu da kuma Sanata Ovie Omoagege.

Sanatan ya jaddada cewa samun nasarar jam'iyyar APC a babban zaben kasa na da babbar nasaba da mashahurancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma al'ummar jihar Kano da suka samar da kimanin kuri'u miliyan 1.4 cikin kuri'u miliyan 6 da yankin Arewa maso Yamma ya samar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel