Wasu muhimman tarihi 4 da Buhari ya kafa a siyasar Najeriya

Wasu muhimman tarihi 4 da Buhari ya kafa a siyasar Najeriya

A yau Laraba, 29 ga watan Mayu ne aka gudanar da bikin rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na biyu a matsayin shugaban kasar Najeriya bayan lashe zaben shugaban kasa na watan Feburairun 2019 da kuri’u fiye da miliyan goma sha biyar.

A yayin da shugaba Buhari ya amshi rantsuwa, Legit.ng ta gudanar da wani bincike akan tarihinsa, inda ta binciko wasu muhimman ababen tarihi guda hudu da Buhari ya kafa a siyasar Najeriya kamar haka;

KU KARANTA: Babu aiki ranar Laraba saboda za’a rantsar da Buhari karo na biyu – Gwamnati

- Dan arewa na farko daya fara mulkar Najeriya sau 3

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa tarihi a matsayin dan Arewa daya tilo daya fara mulkar Najeriya sau uku, mutum daya ne ya taba kafa irin wannan tarihi, watau tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Buhari ne kadai dan Arewa daya taba mulkar Najeriya a karkashin mulkin Soja 1983-1985, sa’annan ya sake mulkar kasar a karkashin tsarin Dimukradiyya daga 2015 zuwa 2019, gashi a yau ya amshi rantsuwar daurawa daga 2019 zuwa 2023 da ikon Allah.

Wasu muhimman tarihi 4 da Buhari ya kafa a siyasar Najeriya
Wasu muhimman tarihi 4 da Buhari ya kafa a siyasar Najeriya
Asali: Facebook

- Shugaban kasan da bai tsige ministansa ko daya ba

Tun bayan dawowar Najeriya bisa tafarkin mulki dimukradiyya a shekarar 1999, ba’a taba samun wani shugaban kasa cikin shuwagabanni hudu da kasar tayi da bai tsige ministansa ko daya ba sai Buhari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kadai wanda bai sallami minista ko daya daga gwamnatinsa ba, sai dai akwai ministocin da suka ajiye aiki don kashin kansu sakamakon cigaba da suka samu.

- Dan arewa na 3 daya zarce a mukamin shugaban kasa

Da wannan rantsarwar da aka ayi ma shugaba Buhari a yau, ya shiga jerin yan Arewacin Najeriya da suka shugabanci Najeriya, kuma suka zarce akan mulki bayan sake lashe zabe.

Dan Arewan daya fara yin tazarce a karagar mulki shine Sir Abubakar Tafawa Balewa, tsohon firai ministan Najeriya, sai kuma marigayi Alhaji Shehu Shagari.

- Shugaban da aka taba rantsarwa cikin watan Azumi

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake kafa wani tarihi a matsayin shugaban kasar da aka taba rantsar dashi a cikin wata mai alfarma, watan Ramadana, tun bayan dawowar Najeriya tafarkin Dimukradiyya a shekarar 1999.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel