A ranar 29 ga watan Mayu za a rantsar da shugaban kasa Buhari

A ranar 29 ga watan Mayu za a rantsar da shugaban kasa Buhari

Domin kawar da shakku da kuma watsi da rade-radi wajen bayyana tabbas, gwamnatin tarayyar Najeriya ta fayyace ranar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi rantsuwa ta riko da akalar jagorancin kasar nan a wa'adin sa karo na biyu.

Kamar yadda aka dabbaka a baya, gwamnatin tarayya ta ce shugaban kasa Buhari zai yi rantsuwa ta karbar ragamar jagorancin kasar nan a ranar 29 ga watan Mayu sabanin yadda ake ikirarin sauya ranar zuwa 12 ga watan Yuni.

Mallam Garba Shehu
Mallam Garba Shehu
Asali: UGC

Babban hadimi na musamman ga shugaban kasa Buhari a kan sadarwa da kuma hulda da al'umma, Mallam Garba Shehu, shi ne ya yi wannna karin haske yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin cikin fadar Villa da ke garin Abuja.

A makon da ya gabata rahotanni daga kafofin sadarwa sun haskaka cewa, shugaban kasa Buhari zai karbi rantsuwa ta jan ragamar jagorancin kasar nan a ranar 12 ga watan Yuni a yayin da gwamnatin kasar ta kaddamar tare da mai she ta sabuwar ranar Dimokuradiyya.

Sai dai hadimin na shugaban kasa cikin furucin sa na fashin baki ya ce, za rantsar da shugaban kasa Buhari a ranar 29 ga watan Mayu kamar yadda aka dabi'antu a baya. Kazalika sabuwar ranar karbar rantsuwa za ta ci gaba da tasiri a wa'adi na gaba.

KARANTA KUMA: Domin na kasance jakadan zaman lafiya ya sanya zan hakura da kujerar Sanata - David Mark

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Mallam Garba ya ce masu hannu cikin yada wannan jita-jita ba su da wata manufa illa iyaka kawo rudani a cikin al'umma.

Shugaban kasa Buhari ya sauya ranar dimokuradiyyar kasar nan daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni domin karamci da kuma tabbatar da nasarar Marigayi MKO Abiola a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel