Buhari ya yi ganawar sirri da wasu gwamnoni uku

Buhari ya yi ganawar sirri da wasu gwamnoni uku

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri a lokuta daban-daban da gwamnan jihar Legas; Akinwunmi Ambode, na jihar Kaduna, Malama Nasir El-Rufa'i, da kuma na jihar Benuwe; Samuel Ortom.

Dukkan gwamnoni sun gana ne da Buhari a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu.

Babu wani jawabi da fito dangane da dalilin ziyarar da gwamnoni suka kai wa Buhari ba, kazalika ba samu labari a kan abinda suka tattauna ba.

Kafin ya karbar bakuncin gwamnonin, Legit.ng ta sanar da ku cewar gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele, ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin.

Cikin murmushi da annashuwa, Emefiele ya gaisa da shugaba Buhari a lokacin da shugaban kasa ke taya shi murna.

A cikin satin da ya gabata ne shugaba Buhari ya sake aike wa da sunan Emefiele zuwa majalisa domin sake amince wa da shi a matsayin babban gwamnan CBN a karo na biyu.

A ranar 29 ga watan Mayu ne za a sake rantsar da shugaba Buhari a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya a karo na biyu, bayan ya lashe zaben da aka yi a watan Fabarairu.

Shugaba Buhari ya ki bayyana sunayen mutanen da zai bawa mukaman siyasa a sabuwar gwamnatinsa.

Sai dai, hakan bai hana gwamnoni da wasu jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar APC yin zawarcin neman shugaba Buhari ya bawa wasu na hannun daman su ko yaran su mukamai ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel