Da duminsa: An sanya dokar hana fita a jihar Bauchi

Da duminsa: An sanya dokar hana fita a jihar Bauchi

- Wani rikici da ya barke tsakanin matasa a jihar Bauchi ya tilasta gwamnatin jihar sanya dokar ta baci na tsawon wani lokaci

- Gwamnatin ta bukaci jama'ar yankin da abin ya shafa akan su bi doka yadda ya kamata, saboda ba za ta ragawa duk wani wanda ta kama yana karya doka ba

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanya dokar ta baci a wasu yankuna na jihar bayan wani rikici da ya kaure tsakanin matasa a jihar.

A wata sanarwa wacce sakataren gwamnatin jihar, Mohammed Nadada Umar ya sanyawa hannu, ya bayyana cewa gwamnatin ta sanya dokar ne bayan rikicin da ya kaure tsakanin wasu matasa ranar Alhamis 9 ga watan Mayu, 2019.

Sanarwar ta bayyana cewa, matasan sun samu sabani da misalin karfe 9 na safe a karamar hukumar Gudum da ke jihar Bauchi, yayin da sabanin ya yi sanadiyyar tada rikici tsakanin matasan Gudum Sayawa da kuma matasan Gudum Hausawa.

Da duminsa: An sanya dokar hana fita a jihar Bauchi

Da duminsa: An sanya dokar hana fita a jihar Bauchi
Source: Depositphotos

Sanarwar ta kara da cewa, matasan sun tada rikici sosai, inda hukumomin tsaro suka shiga tsakani suka kwantar da tarzomar a yankin.

"Sai dai kuma, a lokacin da ake gabatar da sallar juma'a rikicin ya kara tashi, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku," in ji sanarwar da sakataren gwamnatin ya fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa, ta sanya dokar ta bacin ne domin kawo karshen rikicin a yankunan, inda dokar za ta fara aiki da misalin karfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.

KU KARANTA: Wasu abubuwa da Atiku zai yi idan bai samu nasara a kotu ba

Wuraren da dokar za ta shafa sun hada da Gudum Fulani, Gudum Hausawa, Gudum Sayawa da kuma Bigi.

"An bukaci al'ummar yankunan da abin ya shafa da su bi doka. Duk mutumin da aka kama da laifin karya doka zai fuskanci fushin hukuma," sanarwar ta yi gargadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Online view pixel