Atiku ya haramta naira dubu goma goma da Buhari ke rabawa na Trader Moni

Atiku ya haramta naira dubu goma goma da Buhari ke rabawa na Trader Moni

Tsohon dan takarar shugaban kasar Najeriya a inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana tsarin bada tallafin naira dubu goma goma ga talakawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kirkiro na Tradermoni a matsayin wani nau’i na rashawa, kuma haramun ne.

A cewar Atiku, APC ta kirkiri Tradermoni ne da nufin yaudarar yan Najeriya su bata kuri’u a zaben shugaban kasa daya gudana a ranar 23 ga watan Feburairu, sa’annan ya kara da cewa babu tanadin kudin Tradermoni a kasafin kudin 2018.

KU KARANTA: Domin tsaro ba don tsoro ba: Babu sallar Tahajjud babu Ittikafi a Masallacin Sultan Bello

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Atiku ya bayyana haka ne cikin korafin daya shigar gaban kotun sauraron korafe korafen zaben shugaban kasa ta hannun lauyoyinsa inda yake kalubalantar nasarar Buhari, tare da buktar kotun ta sanar dashi a matsayin halastaccen shugaban kasa.

“A kokarinsu na yaudarar masu zabe, Buhari yayi amfani da damarsa ta shugaban kasa ya kaddamar da wani tsari mai suna Trader Moni, inda a ciki aka raba ma kananan yan kasuwa N10,000 a duk jahohi 36 na Najeriya, har da FCT Abuja, yayin daya rage yan makonni a yi zabe.

“Duk da cewa babu wani tanadi da gwamnatin tayi a kasafin kudin 2018 na yin wannan aiki, duk da cewa jama’a da dama sun koka kan wannan yaudara, amma shugaban kasa ta hannun mataimakinsa ya cigaba da raba wadannan kudade, suna sayen kuri’u da kudin gwamnati.” Inji shi.

Sai dai shima shugaban kasa Buhari ya mayar da martani ta bakin lauyansa, Wole Olanipekun, wanda ya bayyana ma kotun a rubuce cewa Trader Moni halastaccen tsari ne da aka bullo dashi don taimakon masu karamin jari, don don sayen kuri’u ba.

Har yanzu dai kotun bata sanya ranar fara sauraron karar da Atikun ya shigar ba, inda babban bukatarsa shine ta kwace mulki daga hannun Buhari ta mika masa, saboda a cewarsa shine halastaccen shugaban kasar Najeriya duba da alkalumman sakamakon zabe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel