An kama wadanda suka sace Hakimin Daura

An kama wadanda suka sace Hakimin Daura

- A wani rahoto da muka samu yau Juma'ar nan ya nuna cewa an kama wasu daga cikin barayin da suka sace Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar

- Sai dai kuma har ya zuwa yanzu ba a tabbatar da inda Hakimin ya ke ba

'Yan sandan jihar Katsina sun kama wadanda ke da hannu a sace Alhaji Musa Umar, Hakimin Daura, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman a fannin sadarwa Lauretta Onochie ita ce ta bayyana hakan jiya a shafinta na Twitter.

"Yan sandan jihar Katsina sun ce sun kama wadanda suka sace Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar, wanda suka je har gida suka sace shi," in ji ta.

An kama wadanda suka sace Hakimin Daura

An kama wadanda suka sace Hakimin Daura
Source: UGC

Barayin sun je gidan Hakimin a Daura da misalin karfe 7 na daren Larabar nan da ta gabata, in suka dinga harbe-harbe ba bu kakkautawa.

Hakimin ya dawo daga masallaci kenan, bayan kammala sallar magariba, sai barayin suka kama shi.

Hakimin wanda aka ce siriki ne ga babban dogarin shugaban kasa Muhammadu Buhari, 'yan fashin sun kama shi a kofar gidan shi a daidai lokacin da ya ke hira da wasu mutane.

KU KARANTA: Surukin Dogarin Buhari: 'Yan Sanda sun yi alkawarin bayar da miliyan biyar ga wanda ya kawo labari

Wani shaida ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa barayin sun zo gidan a mota mai kirar Peugeot 406.

An kama wadanda ake zargin, bayan sunyi musayar wuta da jami'an rundunar 'yan sanda "Operation Puff Arder".

Har ya zuwa yanzu dai ba a tabbatar da inda Hakimin ya ke ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel