Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da babban Malamin Izala a Katsina

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da babban Malamin Izala a Katsina

Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da fitaccen mahaddacin Al-Qur’ani, kuma babban Malami a kungiyar Jama’til Izalatil Bidi’a a Iqamatissunnah, Sheikh Ahmad Sulaiman, kamar yadda kungiyar mahaddata Al-Qur’ani ta kasa ta bayyana.

Legit.ng ta ruwaito kungiyar mai suna JIBWIS National Qur’anic Reciters ta bayyana wannan labari ne a shafinta na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda ta ruwaito surukin Malamin, Isma’il Maiduguri wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.

KU KARANTA: Babban dalilin da yasa nake kira a zabi Ganduje – Inji Sheikh Kabiru Gombe

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da babban Malamin Izala a Katsina
Ahmad
Asali: UGC

A jawabinta, kungiyar ta ruwaito Alaramma Isma’il ya bayyana cewa yan bindiga sun yi garkuwa da Sheikh Ahmad Sulaiman ne tare da yan rakiyarsa a hanyar dawowarsu daga jahar Kebbi, a daidai tsakanin kauyen Sheme da Kankara ta jahar Katsina, a daren Alhamis.

“Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da sirikina Alaramma Ahmad Sulaiman da yan rakiyarsa guda 5 a daren jiya, tsakanin Sheme da Kankara dake jahar Katsina, kan hanyar dawowarsu daga Kebbi.” Inji shi.

Daga karshe alaramma Isma’il yayi addu’ar Allah Ya kubutar da Malamin, muma daga nan muna taya Alaramma Ahmad Sulaiman da addu’ar Allah Ya tseratar dashi, muma Ya tseratar damu daga sharrin azzalumai, Amin.

A wani labarin kuma Babban Malamin addinin Musulunci, kuma sakataren kungiyar Jama’atil Izalatil Bidi’a wa Iqamatissunnah, Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana wata kwakkwaran dalilin da ya kamata jama’an jahar Kano su sake zaban Gwamna Abdullahi Ganduje a karo na biyu.

Malamin ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da yayi kuma aka nada, da a yanzu haka yake yawo a kafafen sadarwar zamani ana watsa shi, inda yace babban dalilin da zai fada ma Allah idan Ya tambayeshi akan me yace a zabi Ganduje shine Musuluntar da Maguzawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel