Sunayen mutanen da zasu tsara shagulgulan da za’ayi a bikin rantsar da shugaban kasa Buhari

Sunayen mutanen da zasu tsara shagulgulan da za’ayi a bikin rantsar da shugaban kasa Buhari

Yayin da ake dakon jiran ranar 29 ga watan Mayu don rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya karo na biyu, shugaba Buharin ya sanar da nada kwamitin da zata tsara yadda za’a gudanar da bikin rantsarwar tasa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya nada sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a matsayin wanda zai jagoranci wannan muhimmin kwamitin, kamar yadda sanarwa daga ofishin babban sakataren ayyukan gama gari, Olusegun Adekunle ya nuna.

KU KARANTA: Adadin yan majalisun da jam’iyyun APC da PDP suke dasu a majalisar wakilai

Sunayen mutanen da zasu tsara shagulgulan da za’ayi a bikin rantsar da shugaban kasa Buhari
Shugaban kasa Buhari
Asali: UGC

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Ministan al’adu da watsa labaru, Lai Muhammed, Ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau, Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, Ministan Abuba, Muhammed Bello, da shugaban jam’iyyar APC ta kasa.

Babban aikin da Buhari ya baiwa wannan kwamiti shine “Tsarawa da aiwatar da duk wasu shagulgulan da ake yi a lokacin rantsar da shugaban kasa, tare da shigar da duk wasu mutane ko kungiyar da suka kamata cikin shirin don tabbatar da nasarar shagalin.”

Sanarwar ta kara da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da kansa zai rantsar da kwamitin a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris a fadar shugaban kasa, Aso Rock Villa dake babban birnin tarayya Abuja.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo shugaban wani kwamitin bincike daya kafa domin gudanar da cikakken bincike akan ayyukan da gwamnatin tarayya take gudanarwa, da kuma duk tsare tsaren data kirkiro.

Ofishin sakataren gwamnatin tarayya ce ta sanar da haka a ranar Talata, 12 ga watan Maris, inda tace Buhari ya shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari don yayi aiki tare da Osinbajo a wannan kwamiti.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel