Kotu ta shafe dukkan tuhume-tuhumen da ake wa marigayi Alex Badeh

Kotu ta shafe dukkan tuhume-tuhumen da ake wa marigayi Alex Badeh

Wata babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta dakile dukkan tuhume-tuhumen badakalar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ke yi wa marigayi tsohon ministan tsaro, Alex Badeh.

Babban Mai Shari’a Okon Abang ya soke karar da tuhume-tuhumen a cikin hukuncin da ya bayar, wanda aka samu kamfanin Badeh mai suna Iyalikam Nigeria Limited da shi Badeh din kan sa da aikata laifukan da aka caje shi.

Ana tuhumar sa ne da laifuka 10 da suka jibinci wawurar kudaden makamai a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Kotu ta shafe dukkan tuhume-tuhumen da ake wa marigayi Alex Badeh
Kotu ta shafe dukkan tuhume-tuhumen da ake wa marigayi Alex Badeh
Asali: Twitter

Kotu ta umarci cewa dukkan gidajen da aka samu a hannun Badeh, a mallaka su ga gwamnatin tarayya ta hannun EFCC.

Mai Shari’a ya kuma ci gaba da cewa a shaida wa Hukumar Rajistar Masana’antu da Kamfanoni ta Kasa wannan hukunci da kotun ta yanke.

KU KARATA KUMA: Sarakunan gargajiya sun kai ma Buhari gaisuwar jinjina da ban girma a Villa (Hotuna)

A wani lamari na daban, mun ji cewa hukumar EFCC ta sanar da sakin wani jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Tanimu Turaki, babban lauyan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, kuma mataimakin yakin neman zaben Atiku na mukamin shugaban kasa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Litinin, 4 ga watan Maris ne EFCC ta cafke Turaki, wanda ya nemi takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, amma Atiku ya kadashi, sa’annan ya taba zama ministan ayyuka na musamman a gwamnatin Jonathan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel