Assha: Marin uwar miji da keta mata riga ya jefa wata mata cikin tsaka mai wuya

Assha: Marin uwar miji da keta mata riga ya jefa wata mata cikin tsaka mai wuya

- Wata mata mai shekaru 28 mai suna Amaka Okolie ta gurfana gaban kotu bisa zarginta da marin uwar tsohon mijinta tare da lalata mata sarkarta ta N190,000

- Sai dai Okolie ta ce ba ta aikata laifuka biyu da ake zarginki da ake aikatawa ba, wanda suka hada da cin zarafi da lalata dukiya

- Kotun ta bayar da belin Okolie akan N50,000 da wakili guda daya tare da dage shari'ar har sai ranar 20 ga watan Maris, domin ci gaba da sauraron karar

Wata mata mai shekaru 28 mai suna Amaka Okolie wacce aka yi zargin ta mari uwar tsohon mijinta tare da lalata mata sarkarta ta N190,000 a yayin da suka cacar baki a ranar Litinin, ta gurfana gaban wata kotun majistire da ke Ikeja, jihar Legas.

Okolie, wacce ke zaune a gida mai lamba 4, titin Taiwo, Mafoluku a Oshodi, jihar Legas, ta gurfana gaban kotun ne bisa zarginta da aikata laifuka biyu da suka hada da cin zarafi da lalata dukiya. Sai dai ta karyata wannan zargi da ake yi mata.

Jami'i mai shigar da kara ya yi ikirarin cewa wacce ake zargin ta mari tsohuwar surukarta, Mrs Ngozi Okolie, inda har ta yaga mata kayanta tare da tsinka mata sarkarta da kudinta ya kai N190.000, a yayin da suka cacar baki kan gazawar matar na barin gidan mijin surukuwar.

KARANTA WANNAN: Yadda karamar hukumar cikin garin maiduguri ta tarawa Buhari kuri'u mafi yawa a Nigeria

Babbar magana: Marin uwar miji ya jefa wata mata cikin fushin kotu
Babbar magana: Marin uwar miji ya jefa wata mata cikin fushin kotu
Asali: Depositphotos

Sajen na rundunar 'yan sanda, Michael Unah ya shaidawa kotu cewa wacce ake zargin ta aikata laifin ne a ranar 18 ga watan Fabreru, da misalin karfe 8:40 na safe a cikin gidanta.

Ya ce laifin da ta aikata ya ci karo da sashe na 173 da 339 na cikin dokar aikata laifuka ta jihar Legas da aka sabunta a 2015.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa dukkanin laifukan da ake zargin matar da aikatawa, na da hukuncin shekaru shida a gidan yari.

Alkalin kotun, A. A Fashola, ya bayar da belin wacce ake zargin akan N50,000 da wakili guda daya, wanda ke aiki a jihar Legas tsawon shekaru biyu, kuma kotu sai ta amince da adireshinsa.

Alkalin ya dage shari'ar har sai ranar 20 ga watan Maris, domin ci gaba da sauraron karar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel