Zaben 2019: Ingila ta taya Buhari murnar lashe zabe

Zaben 2019: Ingila ta taya Buhari murnar lashe zabe

Gwamnatin kasar Ingila ta taya shugaba Muhammadu Buhari murnar sake lashe zabe kato na biyu a matsayin shugaban kasar Najeriya.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin jakadancin Ingila da ke Abuja ta ce Minista na Africa, Harriett Baldwin ta ce, "Ina mika sakon taya murna ta ga Shugaba Buhari bisa nasarar da ya samu na lashe zabe a matsayin shugaban Najeriya.

"Ingila kasa ce da ta dade tana da alaka mai kyau da Najeriya da al'ummar Najeriya domin su amfani Africa da duniya baki daya."

Baldwin ta yabawa 'yan Najeriya kan jajgircewarsu wurin tabbatar da demokradiyya.

DUBA WANNAN: Ku amince da rashin samun nasara - Gwamna Abubakar ya shawarci Atiku da PDP

Ingila ta taya Buhari murnar lashe zabe
Ingila ta taya Buhari murnar lashe zabe
Asali: Twitter

Ta ce sakamakon zaben da INEC ta sanar ya yi dai-dai da wanda Civil society Parallel Vote ta tattara.

"Muna sa ran 'yan Najeriya za su amince da sakamakon zaben."

Sai dai duk da hakan ta ce wasu 'yan Najeriya sun bayyana damuwarsu a kan rashin kai kayan aikin zabe a kan lokaci, tattara zabe da kuma barazana da jami'an tsaro suka yiwa masu zabe.

"Muna kira ga hukumomin tsaro na Najeriya suyi bincike a kan zargin laifukan da ake zargin aikatawa a kuma dauki mataki da ya dace."

Ta kuma mika ta'aziyarta ga iyalan wadanda suka rasu wurin zaben.

"Bai dace wani ya rasa ransa ba a wurin kada kuri'a," inji ta.

Ta kuma ce Ingila za ta cigaba da tallafawa Najeriya wurin karafafa demokradiyarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel