Kafin karfe 12 na ranar Asabar PDP ta kada APC - Adam A. Zango

Kafin karfe 12 na ranar Asabar PDP ta kada APC - Adam A. Zango

Fitaccen jarumin nan kuma mawaki a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood Adam A. Zango yayi hasashen cewa a ranar Asabar din da ke tafe kafin karfe 12 na rana dan takarar shugabancin kasar Najeriya a PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zabe.

Jarumin dai ya bayyana hakan ne a shafin sa na dandalin sada zumunta na Facebook inda ya rubuta cewa: "Tun 12 Na Rana PDP Zata lashe Zabe", kuma wakilin kafar labaran Legit.ng ta gani.

Kafin karfe 12 na ranar Asabar PDP ta kada APC - Adam A. Zango

Kafin karfe 12 na ranar Asabar PDP ta kada APC - Adam A. Zango
Source: Facebook

KU KARANTA: Diyar Buba Galadima ta je kamfe din Buhari

Tuni dai kalaman na jarumin suka soma tayar da kura tare da haifar da zazzafar muhawara a shafin nasa inda wasu da yawa ke goyon bayan kalaman nasa wasu kuma na yi masa tofin Allah-tsine game da hakan.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jarumin Adam A. Zango ya sauya akalar siyasar sa a kwanakin baya inda ya bar tafiyar shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC ya koma bangaren dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar.

Haka zalika ma Daya daga cikin fitattun fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Maryam Gidado wadda aka fi sani da Maryam Babban Yaro ta bi bayan jarumi Adam A. Zango inda ta bayyana goyon bayan ta ga jarumin game da sauya shekar da yayi a siyasance.

A cewar ta, ko kusa bai kamata mutane su ga laifin jarumin ba domin kuwa kowa yanayin siyasa ne domin ya samu wani abu kuma ya samu kima da daraja musamman ma a wurin mutanen da ake yi domin su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel