An kamo mugayen samarin nan da suka danne budurwa a bidiyo, suka saka mata yaji ta qasa

An kamo mugayen samarin nan da suka danne budurwa a bidiyo, suka saka mata yaji ta qasa

- 'Yan sanda sun kama wasu mutane da suka tozarta wata mata ta hanyar watsa bidiyon ta

- Sun sanya matar tayi tsarki da barkono sannan suka dauketa a tsirara

- Mutane sun nemi hukumar yan sanda data binciko wadanda sukayi mata wannan ta'asa

An kamo mugayen samarin nan da suka danne budurwa a bidiyo, suka saka mata yaji ta qasa

An kamo mugayen samarin nan da suka danne budurwa a bidiyo, suka saka mata yaji ta qasa
Source: Depositphotos

Jami'an yan sanda a jihar Edo sun bayyana cewa sun samu nasarar kama mutanen da suka tozarta wata mata bisa bidiyon ta da suka yada.

Bidiyon yana nuni da yanda yan fashin suka sanya mata barkono a gaban ta sannan suka sukayi mata bidiyo tsirara.

Mutanen sun turmuza mata barkonon inda take ihun neman taimako sannan tana rokar su dasu dena.

Wannan bidiyo ya dauki hankula da dama wanda ya hada ciki da wajen Najeriya inda mutane suka nemi jami'an yan sanda dasuyi bincike akai daga karshe aka gano cewa yan Najeriya ne sukayi wannan ta'asar.

A ranar Alhamis ne hukumar yan sanda ta bayyana cewa ta samu nasarar kama wasu daga cikin wadannan mutane sannan tana cigaba da bincike domin gano ragowar.

GA WANNAN: Gwamna Nasir da Isa Ashiru sun sanya hannu kan takardan lumana gabanin zabe

"Wannan bincike ya bada damar kamo mutane Shida daga cikin wadanda suka tozarta wata mata.

Biyo bayan afkuwar wannan abu kwamishinan yan sanda IGP Muhammed Adamu ya bada umarnin fadada bincike akan lamarin.

Hukumar yan sandan sun bayyana cewa matar da akayiwa wannan abu yar shekaru 24 a halin yanzu ana bincikar lafiyar ta.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel