Yau wata rana: Sarki Muhammadu Sunusi ya cire ma Buhari hula game wani muhimmin aiki da yake yi

Yau wata rana: Sarki Muhammadu Sunusi ya cire ma Buhari hula game wani muhimmin aiki da yake yi

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya bayyana jin dadinsa, tare da jinjina ma shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa kokarin da yake yi game da yaki da fatara da talauci a Najeriya, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sarkin ya bayyana haka ne yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai masa ziyara a fadarsa dake cikin birnin Kano a ranar Alhamis, 31, ga watan Janairu, inda yace ya yaba da tsare tsaren yaki da fatara da Buhari ya kirkiro.

KU KARANTA: An kaure da cacar baki tsakanin Ummi Zee Zee da Zaharaddeen Sani tare da nuna ma juna yatsa

Yau wata rana: Sarki Muhammadu Sunusi ya cire ma Buhari hula game wani muhimmin aiki da yake yi

Buhari a Kano
Source: Facebook

“Shirye shirye irinsu N-Power, da tallafin yan kasuwa na N500 zasu taimaka matuka wajen habbaka tattalin arzikin kasa, don haka ina kira ga gwamnati ta duba yiwuwar kara adadin mutanen dake cin gajiyarsu zuwa miliyan 20.

“Tabbas yin hakan zai taimaka gaya wajen rage radadin talauci daya dabaibaye jama’an Najeriya, haka zalila wannan mataki zai kawo karshen barace baracen kan titi da jama’anmu suke yi.” Inji shi.

Yau wata rana: Sarki Muhammadu Sunusi ya cire ma Buhari hula game wani muhimmin aiki da yake yi

Buhari
Source: Facebook

Haka zalika Sarkin ya bayyana farin cikinsa da tsarin ciyar da daliban makarantun firamari da gwamnatin Buhari ta kirkiro, inda yace ciyarwar za ta taimaka wajen kara adadin daliban makarantun, saboda iyaye da dama zasu gwammace su turasu makaranta ko don abincin.

Sarkin ya jaddada manufar masarautar Kano ta cigaba da tuna ma gwamnatin alkawurran data daukan ma yan Najeriya, tare da bata karin gwiwa da shawarwari a duk lokacin da bukatar haka ta tashi.

Shima a nasa jawabin, shugaba Buhari yace bai je jahar Kano da nufin yakin neman zabe ba kadai ba, amma dalilin bayyana gadiyarsa ga Kanawa bisa gudunmuwar da suke bashi tare da gwamnatinsa.

“Na shigo Kano ne da nufin bayyana ma jama’an Kano ayyukan da muke yi don cigaban Najeriya, haka zalika na yi amfani da daman don tuna musu bukatar su zabi yan takarar da suka cancanta, na fadi haka ne saboda na san irin abinda muke yi.” Inji shi.

Daga karshe Buhari ya bayyana ma godiyarsa ga dubun dubatan jama’an Kanawa da suka tarbeshi a fadar Sarkin Kano, sa’annan ya basu tabbacin zai ciyar da kasar zuwa mataki na gaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel