Damu-dumu: An kama wani babban jami'in gwamnatin Jigawa yana lalata fostocin jam'iyyar adawa, hoto

Damu-dumu: An kama wani babban jami'in gwamnatin Jigawa yana lalata fostocin jam'iyyar adawa, hoto

An dauki hoton wani mai bawa gwamnan jihar jigawa shawara na musamman a kan hulda da jam'iyyun siyasa, Bala Idi yana lalata fostocin dan takarar gwamna na jam'iyyar Social Democratic Party, SDP, Bashir Adamu a karamar hukumar Kazaure da ke jihar Jigawa.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a yayin da Gwamna Mohammed Badaru ke hanyarsa zuwa na zuwa kamfen daga masarautar Hadejia zuwa Gumel sannan ya karasa Kazaure.

A cewar wani shaidan ganin ido da ya nemi a boye sunansa, manyan jami'an gwamnatin Badaru sunyi kaurin suna wurin musguwanawa jam'iyyun hamayya a jihar musamman lokacin kamfen.

An nadi hoton wani jigo a gwamnatin Jigawa yana lalata fostocin jam'iyyun adawa
An nadi hoton wani jigo a gwamnatin Jigawa yana lalata fostocin jam'iyyun adawa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jigo a jam'iyyar APC ya fadi su waye ke tsoron tazarcen Buhari

"Kafin gwamnan ya iso karamar hukumar, Shugaban karamar hukumar da wasu manyan jami'an gwamnati sun sanya 'yan bangar siyasar su lalata fostoci da allunan zabe da jam'iyyun hamayya suka saka.

"Shugaban karamar hukuma da tsohon kwamishinan ayyuka da gidaje a jihar da ya koma APC, Baba Santali sun dauki hayar 'yan daba da ke musu aiki.

"Yan daban sun kasance suna yin barazana ga sauran matasa da ke yiwa jam'iyyun adawa kamfen," inji majiyar.

A yayin da ya ke zantawa da majiyar Legit.ng, dan takarar gwamna na SDP, Mr Adamu ya koka kan yadda gwamnan jihar da mukarrabansa suke amfani da 'yan daba domin yin barazana ga kamfen dinsa.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Abdul Jinjiri ya ce ya samu korafi a kan afkuwar lamarin kuma ya yi alkawarin gudanar da bincike domin gano wadanda suke aikata barnar domin su fuskanci hukunci.

Ya kuma tabbatarwa 'yan takarar jihar cewa ba zai bawa wata jam'iyya fifiko ba wurin zartas da hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel