Babu irin ta’asar da Obasanjo bai yi ba a lokacin yana mulki – Daiyabu

Babu irin ta’asar da Obasanjo bai yi ba a lokacin yana mulki – Daiyabu

Shugaban jam’iyyar adawar nan ta AD watau Alliance for Democracy tayi kaca-kaca da Olusegun Obasanjo. Jam’iyyar tace tsohon shugaban kasar bai da hurumin sukar gwamnatin Muhammadu Buhari.

Babu irin ta’asar da Obasanjo bai yi ba a lokacin yana mulki – Daiyabu
Ana zargin Obasanjo da aikata zunubai sama da 100 a lokacin sa
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Alhaji Abdulkarim Daiyabu wanda shi ne shugaban jam’iyyar AD na kasa baki daya, ya caccaki Cif Olusegun Obasanjo game da wasikar da ya rubuta kwanan nan yana mai sukar shugaban kasa Buhari.

Abdulkarim Daiyabu yake cewa a lokacin Obasanjo yana rike da kasar nan, sai da ya aikata manyan laifuffuka masu girma fiye da 120. A cewar babban ‘dan siyasar, kowane laifi ya isa ya sa a tsige shugaban kasar a lokacin.

Abdul Daiyabu yake cewa duk da irin ta’adin da Obasanjo ya aikata, maimakon majalisa ta tsige sa, sai dai ma aka rika neman hanyar da za a ba shi damar ya zarce a karo na uku. A karshe tsohon shugaban kasar bai ci nasarar haka ba.

KU KARANTA: Masu neman shugaban kasa sun yi wa Obasanjo rubdugu

Alhaji Daiyabu yace a lokacin Obasanjo da mulkin PDP ne Najeriya ta samu makudan kudin da ba a taba ganin irin su ba, amma babu wasu ayyukan da za a gani a kasa. Daiyabu ya kuma zargi Obasanjo da sace kudin gyara lantarki.

Shugaban jam’iyyar ta AD yace PDP ta shirya murde zaben bana ne don haka ta ke kukan cewa INEC na hada kai da jam’iyyar APC mai mulki wajen ganin an tafka magudi. A karshe yayi kira ga jama’a su marawa shugaba Buhari baya.

Yanzu haka dai Abdulkarim Daiyabu yana cikin masu yakin tazarcen shugaba Muhammadu Buhari a APC, yayi kira ga jama’a su yi watsi da sabuwar wasikar da Obasanjon ya rubuta wannan karo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel