2019: Ba za muyi aiki da na'urar 'Card Reader' ba wajen aikewa da sakamakon zabe - INEC

2019: Ba za muyi aiki da na'urar 'Card Reader' ba wajen aikewa da sakamakon zabe - INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta tarayyar Najeriya wato INEC ta ce za ta yi amfani da na'urar nan dake tantance 'yan takara watau 'Card Reader' a turance a zabukan da ake shirin yi a watannin Faburairu da Maris na wannan shekarar ta 2019.

To amma sai dai hukumar har ila yau ta bayyana cewa ba za a yi amfani da na'urar ba wajen aikewa da sakamakon zaben da za'a gudanar daga rumfunan zabe zuwa hedikwatarta dake Abuja kai tsaye kamar yadda jam'iyyar PDP ta bukata a takarda kamar a 2015.

2019: Ba za muyi aiki da na'urar 'Card Reader' ba wajen aikewa da sakamakon zabe - INEC
2019: Ba za muyi aiki da na'urar 'Card Reader' ba wajen aikewa da sakamakon zabe - INEC
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kiristocin Kano sun fadi wanda za su zaba a 2019

Legit.ng Hausa ta tsinkayi mai magana da yawun hukumar, Mallam Aliyu Bello yana cewa ganin yadda na'urar ta taimaka wajen gudanar da sahihin zabe a shekarar 2015, ya sa a yanzu ma za a yi amfani da ita.

Mallam Aliyu Bello ya ce a cikin shirye-shiryen da hukumar ke yi don ganin an yi sahihin zabe, ta kara inganta sauri da kuma nagartar na'urar yadda ba za a samu wata matsala ba.

Ana dai amfani da na'urar Card Reader ne wajen tantance katin zaben masu kada kuri'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel