Dalilai 9 da suka haddasa talauci a Arewacin Najeriya - Shehu Sani

Dalilai 9 da suka haddasa talauci a Arewacin Najeriya - Shehu Sani

Daya daga cikin mafi shaharar Sanatocin Najeriya, Shehu Sani, mai wakilcin shiyyar Kaduna ta Tsakiya a zauren majalisar dattawa ta Najeriya, a bisa mahanga da fahimtar sa, ya wassafa wasu dalilai da suka sanya talauci ya yiwa Arewacin Najeriya katutu.

Sanatan shiyyar Kaduna ta Tsakiya; Sanata Shehu Sani

Sanatan shiyyar Kaduna ta Tsakiya; Sanata Shehu Sani
Source: Depositphotos

Sanata Shehu cikin wani sako da ya rubuta a shafinsa na zauren sada zamunta na Facebook, ya zayyana cewa, rashin bin tafarki na magabatan kwarai na daya daga cikin dalilai da suka sanya talauci ya zamto tamkar takalmin Kaza a Arewacin Najeriya.

Ya ke cewa, ko shakka ba bu watsi da tafarki na dabi'a da al'ada, mahanga ta tsantseni da tattali da marigayi Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello ya shimfida, na daya daga muhimman dalilai da su haddasa annobar talauci a yankunan Arewa.

KARANTA KUMA: Sabuwar shekara ta 2019 dama ce ga jagorori da mabiya su kyautata rayuwar su - Jonathan

Sakon sanatan da ya rubuta mai taken jerin dalilai 9 da suka sanya talauci ya yi matukar tsanani a Arewacin Najeriya sun hadar da:

1. Watsi da harkar noma tare da dogaro akan man fetur da ma'adanan sa.

2. Watsar da dabi'u da kuma al'adu.

3. Ta'addanci gami da rikici da tarzoma ta fuskar kabilanci.

4. Rashin kalubalantar jagorori da shugabanni da suka rike makogoron talakawa.

5. Tsantsar tsana da hassada ga masu hannu da shuni da ta mamaye zukatan talakawa.

6. Zalunci da acin amanar juna a tsakanain al'umma da kuma shugabanni.

7. Rashin bai wa Arewacin Najeriya muhimmanci tsawon shekaru aru-aru.

8. Durkushewar ilimi musamman a makarantun gwamnati.

9. Tsagwaran yarda da cewa komai kaddara ce.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel