Kungiyoyin matasa sun koka kan yadda ake sakin kudin kamfe ba'a badawa dasu

Kungiyoyin matasa sun koka kan yadda ake sakin kudin kamfe ba'a badawa dasu

- Ana rabon kudi a jam'iyya babu su

- Sunce ana nuna musu wariya da banbanci

- Matasa basu jin dadin yadda APC ke ware su lokutan Kamfe

Kungiyoyin matasa sun koka kan yadda ake sakin kudin kamfe ba'a badawa dasu

Kungiyoyin matasa sun koka kan yadda ake sakin kudin kamfe ba'a badawa dasu
Source: Facebook

Matasa da dama ne suka koka kan sabon list na masu kamfe a jam'iyyar, kwamootoci da jama'u da zasu yi wa jam'iyyar aikin yakin neman zabe, musamman na jihohin Arewa.

Hadakar kungiyoyin matasan, wadanda suke karkashin Comrade Terver Aginde na yankin tsakiyar Arewa, sunce jerin sunayen da aka saki a yau juma'a, ya basu mamaki, inda aka bada mukamai da kayan aiki amma banda matasa.

DUBA WANNAN: Cikuna sun duri ruwa, bayan da Buhari yace zai kakkabe mugayen jihar Kwara kain zabe

An san dai wannan na nufin an sako kudi da masu yi wa jam'iyyar aiki zasu samu su nemo kuri'u, sai dai ba kowa aka baiwa ba, duk da su matasan sune kashin bayan wannan tafiya.

Comrade Terver Aginde yace suna biye, suga yaya lamarin ke tafiya, kuma in ba'a sauya list din ba zasu dauki mataki nan gaba kadan. Zabe dai saura kasa da kwana 50 ayi shi a 2019.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel