Da duminsa: Ina goyon bayan saka dokar ta baci a Zamfara - Gwamna Yari

Da duminsa: Ina goyon bayan saka dokar ta baci a Zamfara - Gwamna Yari

Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya bayyana goyon bayansa ga kirar da shugaba Muhammadu Buhari ya yi na saka dokar ta baci a jihar Zamfara.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa Yari ya ce "Nima ina goyon bayan saka dokar ta baci idan har hakan zai kiyaye rayyuka da dukiyoyin al'ummar jiha ta."

Ya gargadi 'yan siyasa su dena amfani kallubalen tsaro na jihar domin cimma burinsu na siyasa.

Da duminsa: Ina goyon bayan saka dokar ta baci a Zamfara - Gwamna Yari

Da duminsa: Ina goyon bayan saka dokar ta baci a Zamfara - Gwamna Yari
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Da ana kan tsarin gaskiya a Najeriya da tuni kana kurkuku - Buhari ya caccaki Atiku

"Muna magana ne a kan rayyukan al'umma kuma hakan na bukatar a hadu waje guda a hada kai domin kawo karshen lamarin.

"Idan ta doka ta bani damar amfani da makami domin in yaki 'yan ta'addan, da tuni nayi hakan.

"Amma idan bana nan, akwai wasu da ke hadin gwiwa da hukumomin tsaro domin yakar 'yan ta'addan.

"Jami'an tsaro suna iya kokarinsu. Amma abin bakin ciki shine wasu daga cikin wadanda ke da hannu cikin garkuwa da mutane 'yan uwan mutanen da ake garkuwa da su ne wanda hakan na daya daga cikin abinda ya sa matsalar ke da wuyan magancewa.

"Dole sai mun hada kai waje guda mun tona asirin wadanda ke hada baki tare da 'yan ta'addan kuma muyi addu'a Allah ya kawo mana karshen lamarin," inji Yari.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa 'yan ta'addan suna cigaba tsallake duk wani tarko da hukumomin tsaro ke dana musu a matakin jihar da na tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel