Dan Autan Buhari shima ya mika nasa kasafin kudin ga Majalisar jihar dake Lugard Hall

Dan Autan Buhari shima ya mika nasa kasafin kudin ga Majalisar jihar dake Lugard Hall

- Gwamnan jihar Kaduna yasa hannu a kasafin kudin 2019 na jihar Kaduna kamar yanda yan majalisar jihar suka amince

- A lokacin ne kuma aka saka hannu akan kasafin kudin kananan hukumomi 23 na jihar

- Wannan na nuna cewa lokaci daya kananan hukumomi da jihar zasu fara aiyukan shekarar 2019

Dan Autan Buhari shima ya mika nasa kasafin kudin ga Majalisar jihar dake Lugard Hall
Dan Autan Buhari shima ya mika nasa kasafin kudin ga Majalisar jihar dake Lugard Hall
Asali: UGC

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, a ranar juma'a yasa hannu akan kasafin kudin 2019 Naira biliyan 157.44 kamar yadda majalisar jihar ta amince.

Gwamnan ya amince da kasafin kananan hukumomi 23 da ya kai Naira biliyan 62.34.

Majalisar jihar ta kara kasafin kudin kadan zuwa Naira biliyan 155.86. Mista Rufa'i yace duk da gyaran da akayi kasafin kudin jihar na nan a kashi 60 na manyan aiyuka, kashi 40 na kasafin kudin aiyukan lokaci zuwa lokaci.

"A yau wannan gyaran kasafin kudin gwamnatin jihar ya shafi kasafin kudin kananan hukumomi 23 na jihar nan."

A kasafin kananan hukumomi, gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin ta kaddamar da shirin Fiscal Transparency Sustainability and Accountability na kananan hukumomi don duba yanayin aiyuka. Yayi bayanin cewa shirin na kyautatawa kananan hukumomi da suka dau kasafin kudin, kashe su, duba malamai marasa zuwa aiki, ma'aikatan lafiya da sauran su.

DUBA WANNAN: Taliban na iya kwace Afghanista bayan ficewar Amurka

Ya kara da cewa shirin zai fara ne a 2019. "Mun shirya tabbatarwa da kananan hukumomi sunyi aiyukan su don gyaran jiha," Mista Elrufai ya jaddada"

Kamar yanda yace, wannan shine na farko a tarihin jihar da kasafin jihar da na kananan hukumomi aka sa hannu akan su a rana daya.

"Wannan na nufin cewa kananan hukumomin mu, a lokaci daya zasu fara aiyukan shekara da jiha tun daga kirkirar su a 1976." ya rufe.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel