Jam'iyyar APGA na magagin wargajewa gabanin 2019

Jam'iyyar APGA na magagin wargajewa gabanin 2019

- Yan jam'iyyar APGA na ta tururuwar PDP a karamar hukumar Njikoka dake Anambra

- Chief Dan Okpoko ne ya jagoranci yan canjin shekar

- Sunce bazasu iya jure rashin gaskiya irin na jam'iyyar APGA

Jam'iyyar APGA na magagin wargajewa gabanin 2019
Jam'iyyar APGA na magagin wargajewa gabanin 2019
Asali: Depositphotos

Yan jam'iyyar APGA da yawa na karamar hukumar Njikoka dake jihar Anambra sun canza sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Chief Dan Okpoko ne ya jagoranci masu canza jam'iyyar.

Okpoko yace mutane karamar hukumar bazasu cigaba da jure abinda ya kwatanta da rashin gaskiyar shuwagabannin jam'iyyar APGA din ba ballantana yanda sukayi zaben fidda gwani na jam'iyyar.

Yace, "Na shiga jam'iyyar APGA da zuciya daya a shekaru bakwai da suka wuce, amma bayan kankanin lokaci na fara gano yaudara tsakanin shuwagabannin jam'iyyar."

DUBA WANNAN: Dubi yara da yau kotu ta daure don zamba, sai dai manyan barayi suna AC suna jiran a zabe su a gwamnati

"Abun tararrabin shine, muna kokarin cin zabe amma bayan zabe wadanda sukayi kokari gurin samu aci zaben sai a maida su gefe ba a tafiya dasu. Saboda haka ne na yanke shawarar komawa tsohuwar jam'iyyata ta PDP tare da dukkan magoya bayana saboda burina na shiga APGA bai cika ba. "

Okpoko yace yankin Nimo, Abba da Abagana da suka hadu suka bada mazabar Njikoka ta biyu sun yarda a shekarun baya cewa kujerar majalisar dattawa ta dinga zagaye a tsakanin su a duk shekarar zabe.

Yayi dana sanin cewa mahukuntan yankin da kuma APGA sun bata yarjejeniyar da yankin sukayi.

Ya kara da cewa, "Kowa yasan wadanda muka tura majalisar dattawa sunayin shekaru hudu ne sai su dawo su ba wani bangaren yankin damar kai nasu mahukuncin. Yanzu layin yazo kan yankin Abagana zuwa majalisar dattawa kuma ni bazan goyi bayan rashin gaskiya ba saboda mahukuncin yanzu ma daga yankina yake."

"A saboda wannan rashin gaskiyar ta APGA ne zan maida Nimo PDP don yankin ya samu hakkin shi Idan lokacin tura namu wakilin yazo. Bayan haka ma babu wani cigaba da Nimo zata nuna na cewa tana goyon bayan APGA a shekarun nan. Don haka wannan damar mu ce ta samarwa yankin mu yanci ne."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel