Da dumi dumi: Sanatan PDP, Lidani ya sauya sheka zuwa APC

Da dumi dumi: Sanatan PDP, Lidani ya sauya sheka zuwa APC

- Wani sanata a jam'iyyar PDP, Sanata Joshua Lidani, ya sauya sheka daga jam'iyyarsa zuwa jam'iyya mai mulki ta APC

- Lidani, wanda tsohon gwamnan jihar Gombe ne, na wakiltar mazabar Gombe ta Kudu a majalisar dattijai ta kasar

- An zabi sanatan ne a 2015 karkashin jam'iyyar PDP, sai dai ya rasa tikitin tazarcensa na majalisar dattijai a hannun 'yar majalisa Binta Bello

Wani sanata a jam'iyyar PDP, Sanata Joshua Lidani, ya sauya sheka daga jam'iyyarsa zuwa jam'iyya mai mulki ta APC. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Ahmad Lawan (APC, Yobe) sanar da sauya shekar Lidani a zaman da majalisar na ranar Laraba.

Lidani, wanda tsohon gwamnan jihar Gombe ne, na wakiltar mazabar Gombe ta Kudu a majalisar dattijai ta kasar.

An zabi sanatan ne a 2015 karkashin jam'iyyar PDP, sai dai ya rasa tikitin tazarcensa na majalisar dattijai a hannun 'yar majalisa a majalisar wakilai ta tarayya, Binta Bello, wacce ta lashe zaben kujerar a zaben fitar da gwani da ya gabata.

KARANTA WANNAN: Rabon kwado: Kungiyoyin PDP 145 sun bijirewa Atiku, sun koma bayan Buhari da APC

Da dumi dumi: Sanatan PDP, Lidani ya sauya sheka zuwa APC
Da dumi dumi: Sanatan PDP, Lidani ya sauya sheka zuwa APC
Asali: Twitter

A baya bayan nan, Legit.ng Hausa,ta ruwaito maku cewa gamayyar wasu kungiyoyin siyasa sama da guda 145, suka janye goyon bayansu ga jam'iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, kana suka jaddada goyon bayansu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC a zaben 2019.

Da ya ke jawabi a taron kaddamar da mubayi'arsu tare da fara taya Buhari yakin zabe, kodinetan kungiyoyin, Bello Osaretin, ya ce sun yanke wannan hukunci ne don sha'awarsu ta ganin kasar ta kai 'Mataki na gaba'.

A yayin da yake shan alwashin hada kan mambobinsu don baiwa shugaban kasa Buhari kuri'u miliyan shida, kodinetan kungiyoyin ya ce: "Mu gamayyar kungiyoyin da suka fusata da Atiku, muna kan hada kan kungiyoyi 145 a fadin Nigeria, inda kuma muka janye goyon bayanmu ga yakin zaben Atiku Abubakar, tare da jaddada goyon bayanmu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng