Rundunar sojin sama sun yiwa yan Boko Haram luguden wuta a Borno (Bidiyo)
Dakarun sojojin saman Operation LAFIYA DOLE sun yiwa yan ta'addan Boko Haram ruwan wuta a sansaninsu dake Buk, kusa da dajin Alagarno. Wannan ya biyo bayan tura jami'an sojin kasa na musamman domin taimakawa wadanda ke kasa.
Kakakin hukumar sojin saman, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya saki wannan jawabi ne a yau Juma'a, 16 ga watan Nuwamba, 2018.
Yace: " A cigaba da atisayen OPERATION GREEN SWEEP, sashen dakarun saman rundunar Operation LAFIYA DOLE, sun ragargaji sansanin yan Boko Haram da ke Ajigin-Talala, kusa sa djin Algarno, a ranan Laraba, 14 ga watan Nuwamba 2018."
An kai wannan hari bayan binciken da aka gudanar inda aka gano wani sansanin Boko Haram cikin daji mai duhu."
"An tura jirgin Alpha Jet da mai saukar angulun Mi-35 guda biyu inda sukayi lugiden wuta kuma suk tarwatsa sansanin."
KU KARANTA: Kotu ta ragewa tsohon gwamna Dariye wa'adin zaman gidan yari
Mun kawo muku rahoton cewa Babban hafsan ya turo rundunar sojin 123 Special forces din ne wadanda aka sani ba'a amfani da su sai munin rashin zaman lafiya ya yi tsamari, yayinda yayi bayani kan irin nasarorin da hukumar take samu wajen yaki da Boko Haram.
Kalli bidiyon:
Asali: Legit.ng