Yarda da aminci: Kiristoci ma na kai kara wajen 'yan Hisbah a Kano

Yarda da aminci: Kiristoci ma na kai kara wajen 'yan Hisbah a Kano

Kamar yadda kuka sani hukumar Hisbah wata kotun shari’a ce da aka kafa ta kuma tana aiki ne bisa tsarin addinin Musulunci. Wannan hukuma dai ta kasance tana aiki ne a wasu jihohi a yankin arewacin kasar.

Sai dai wani abun mamaki mun samu labarin cewa mabiya addinin Kirista a Kano sun ce sun fi jin dadin kai kokensu gaban 'yan Hisbah maimakon zuwa wajen 'yan sanda, shafin BBC Hausa ya ruwaito.

Komolafe Johnson wanda shi ne shugaban wata kungiyar Kiristoci mai suna 'Humanity Peace and Leadership Synergy Initiative' a Sabon Garin Kano, ne ya bayyana hakan ga majiyarmu.

Yarda da aminci: Kiristoci ma na kai kara wajen 'yan Hisbah a Kano
Yarda da aminci: Kiristoci ma na kai kara wajen 'yan Hisbah a Kano
Asali: Facebook

Ya ce: "Jami'an Hisbah ba sa karbar ko sisi a hannun mutum sannan kuma su kan tabbatar da sun warware matsalar da mutun ya kai gabansu.

"Ba da dadewa ba muka kai wata kara tsakanin wani mai gidan haya Musulmi da dan haya Kirista, kuma sun sasanta su.

"Abin mamakin shi ne sun rika karanto wasu ayoyi daga littafin Babul a lokacin da ake sauraron karar".

Ya kuma ce shekaru da dama kenan yana kai kara zuwa wurin hukumar ta Hisbah kuma a duk tsawon wannan lokacin ba su taba karbar ko kwabo a wurinsa ba.

KU KARANTA KUMA: Na san yadda Boko Haram ya fara – Atiku ya bayyana

Kakakin Hukumar Hisbah, Adamu Yahaya ya ce wannan matakin da wadannan Kiristocin ke dauka ya nuna cewa ba dukkansu ne ke adawa da dokokin Musulunci da ayyukan Hisbah ba.

Sai dai sakataren kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Kano, Ibrahim Isa Wangida ya ce kungiyarsu na adawa da wanna tsarin ba, domin Kiristocin da ke kai kara wajen Hisbah ba za su yarda da hukuncin Hisban ba idan Musulmi suka kai su kara can.

Amma Wangida ya ce suna da kyakkyawar dangantaka tsakaninsu da Hisbah, kuma ba da dadewa ba da wasu yara Kirista suka bata, hukumar Hisbah ce ta gano su kuma ta mika su ga kungiyar CAN kafin daga baya aka mika su ga iyayensu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng