Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi

Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusu II ya bayyana cewa musifar da ta fi na Boko Haram na nan tafe nan da shekaru 20 masu zuwa muddin gwamnati bata inganta tattalin arziki da yawaitar haihuwa ba a arewacin Najeriya.

Sarkin ya yi wannan jawabin na a wata taron kwanaki 3 na kasa da kasa a kan Hanyoyin da za a magance matsalar Boko Haram da akayi a ranar Talata a jihar Kano.

A cewarsa, manyan abubuwan da suka janyo rikice-rikicen Boko Haram sun hada talauci da fatara da ake fama da shi musamman a arewacin Najeriya.

Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi
Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: An rufe wata makaranta a kudancin Najeriya saboda wasu dalibai sun saka Hijab

Sarki Sanusi ya ce adadin matasan da ke Najeriya zai kai miliyan 100 nan da shekaru 20.

Ya kara da cewa muddin gwamnati ta gaza daukan mataki kan yadda mutane ke haihuwa barkatai ba, balo'in da za su bula a kasar za su fi na Boko Haram.

Sanusi da ya wakilci Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad III a taron ya lura cewa yawan haihuwa, inganta ilimi, magance shaye-shayen miyagun kwayoyi suna daga cikin abubuwan da gwamnati za ta magance idan ana son samar da zaman lafiya.

Sarki Sanusi ya shawarci gwamnati ta rika tantance malamai masu wa'azi domin rage yaduwar tsatsauran ra'ayoyi, ya ce ya kamata a rika bayar da lasisin wa'azi ga malamai da aka tantance.

A jawabinsa, gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce gwamnatinsa ta kase fiye da N500 miliyan wajen yaki da kungiyar Boko Haram a jihar.

"Mun sayo da na'urori na zamani tare da daukan nauyin kwarare da ke tattara mana bayanai domin magance Boko Haram a jihar mu," inji Ganduje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel