Shari'ar 11bn: EFCC ta tilasta ni bayar da shaidar karya kan Shema - Lawal Rufai
- Lawal Rufai, ya shaidawa kotun cewa bayanan da EFCC ta gabatar a matsayin hujja kan Shema, ta same su ne ta hanyar tilasta shi sa hannun kan abubuwan da ba gaskiya bane
- Rufai, wanda tsohon babban sakatare ne a ma'aikatar kula da harkokin kananan hukumomi da masarautun gargajiya na jihar, ya bayyana hakan ta bakin lauyansa, Aliyu Ahmed
- Mai shari'ar, Ibrahim Bako, ya dage sauraron karar har sai 28 ga watan Nuwamba don sauraron kara cikin kara
An samu wata 'yar takaddama a ranar jiya, a babbar kotun jiha ta Katsina, a lokacin da Lawal Rufai, daya daga cikin wadanda ake kara tare da tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shehu Shema, ya shaidawa kotun cewa duk wasu bayanai da hukumar EFCC ta gabatarwa kotun a matsayin hujja kan Shema, ta same su ne ta karfin tsiya, da kuma tilasta shi sa hannun kan bayanan da ba gaskiya bane.
Rufai, wanda tsohon babban sakatare ne a ma'aikatar kula da harkokin kananan hukumomi da masarautun gargajiya na jihar, ya bayyana hakan ta bakin lauyansa, Aliyu Ahmed.
A zaman da kotun tayi na baya bayan nan, EFCC ta gabatar da wasu takardun banki a matsayin hujja kan Shema da zata kara tabbatar da zargin rashawa da ake masa, haka zalika lauyoyin masu karar, bisa jagorancin Chief Lateef Fagbemi (SAN), sun bukaci kotun da ta dauki wadannan bayanai a matsayin hujja.
KARANTA WANNAN: Hawainiyarka ta kiyayi ramar Peter Obi - PDP ta ja kunnen El-Rufai

Asali: UGC
A zaman da kotun tayi a jiya, wani jami'in hukumar EFCC, Abubakar Buba, ya shaidawa kotun cewa Rufai ne da kansa ya sa hannu kan dukkanin bayanai da aka samu daga wajensa a shekarar 2016.
Sai dai Ahmed ya karyata wannan ikirari na jami'in hukumar EFCC, inda ya ce "wanda nake karewa, wanda shine shaida na hudu, ya shaida mun cewa duk wasu bayanai da EFCC ta gabatar gaban kotun ta same su ne ta hanyar tilaschi da kuma tursasa shi fadin abubuwan da ba gaskiya bane.
"Da wannan, na ke bukatar wannan kotu mai albarka, da ta sake duba wannan lamari da idon basira, don kuwa hujjojin da EFCC ta gabatar, ta same su ba bisa ka'ida ba, bai kamata kuma a dauke su a matsayin hujja ba."
Mai shari'ar, Ibrahim Bako, ya dage sauraron karar har sai 28 ga watan Nuwamba don sauraron kara cikin kara.
Ana tuhumar tsohon gwamnan jihar Katsina, Shema, tare da wasu mutane uku, da suka hada da tsohon kwamishinan harkokin kananan hukumomi, Sani Makana; tsohon shugaban ALGON, Lawal Dankaba da kuma shi Lawal Rufai, akan aikata laifuka 24 na almubazzaranci da akalla Naira biliyan 11 na kudaden kananan hukumomi.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng