Ba zamu daina bincikan Ganduje ba – Majalisar dokokin Kano

Ba zamu daina bincikan Ganduje ba – Majalisar dokokin Kano

Majalisar dokokin jihar Kano a jiya Talata ta bayyana cewa ba zata daina binciken da ta kaddamar kan gwamnan jihar, Abdullah Ganduje, ban a bidiyoyin karban cin hanci da dan jarida, Jafar Jafar, ya saki a kwanakin nan.

Bayan wadannan bidiyoyi sun bayyana, majalisar dokokin jihar Kano ta kafa kwamiti na musamman domin gudanar da bincike kansa.

Yayinda binciken ke gudana, wata babbar kotu da ke zaune a jihar Kano ta bada umurnin cewa kwamitin binciken da aka nada kan neman gaskiyan al’amarin ta dakatar da bincike.

Wannan ya faru ne sakamakon karar da wata kungiyar lauyoyi ta shigar cewa kafa kwamitin bincike ya sabawa doka.

KU KARANTA: An takaita zirga-zirga a wasu sassan Kaduna saboda shari'ar El-Zakyzaky

A shari’ar alkalin kotun, Jastis A.T Badmasi, ya umurci kwamitin ta dakatar da bincike har sai ya karasa yanke hukuncinsa.

An daga zaman karar zuwa ranan 12 ga watan Nuwamba, domin cigaba.

Amma shugaba kwamitin binciken, Baffa Dan Agundi, ya ce kotun bata umurcesu da dakatad da binciken ba.

A jawabinsa, “Mun samu wasikar kotu kan daina gudanar da bincike kan bidiyon da ya nuna gwamnan Abdullahi Umar Ganduje, na krban cin hanci.”

“Mun tattauna a majalisa yau kuma bisa ga fahimtarm, kotu bata hana mu bincike kan zargin ba, innama kotu ta ce mu cigaba ne, saboda haka zamu cigaba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng