Yanzu yanzu: Agbaje ya zabi daraktar 'First Bank', Haleematu a matsayin abokiyar takararsa
- Jimi Agbaje, dan takarar gwamnan jihar Legas a zaben 2019 da ke gabatowa karkashin jam'iyyar PDP, ya sanar da Mrs. Haleematu Busari, a matsayin abokiyar takararsa
- Mrs. Busari yanzu na aiki a matsayin darakta a bankin 'First Bank', da ke kasar Sierra Leone
- Jimi Agabaje, ya zabi Mrs. Busari ne biyo bayan tattaunawa da tuntubar shuwagabanni da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar
Jimi Agbaje, dan takarar gwamnan jihar Legas a zaben 2019 da ke gabatowa karkashin jam'iyyar PDP, ya sanar da Mrs. Haleematu Busari, a matsayin abokiyar takararsa, (mataimakiyarsa).
Mrs. Busari ta taba rike mukamin darakta a kamfanin layin waya na Zain Nigeria Ltd (wanda ya koma Airtel Nigeria), a yanzu kuma tana aiki a matsayin darakta a bankin 'First Bank', da ke kasar Sierra Leone.
Ta kammala karatun lauyancinta a jami'ar Legas (UNILAG).
KARANTA WANNAN: Abdullahi Ganduje: Mun bunkasa rayuwar matasa 200,000 a cikin shekaru ukku

Asali: Depositphotos
A cikin wata sanarwa da aka bayar a ranar Alhamnmis daga hannun daraktan Jemi Agabaje, na kafofin sada zumunta da watsa labarai na kungiyar yakin zabensa, Felix Oboagwina, ya ce dan takarar jam'iyyar ta PDP ya zabi Mrs. Busari ne biyo bayan tattaunawa da tuntubar shuwagabanni da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar.
"Mrs Oluwayemisi ta samu karbuwa a wajen masu ruwa da tsaki da shuwagabannin jam'iyyar PDP na jihar, kowa yana da yakinin zata kawo gagaruwamar gudunmowa da nasarar wannan kuduri da aka sanya a gaba. Hadaka tsakanin Jimi-Haleemat zai kawo nasara a zaben 2019," a cewar sanarwar.
An haifi Haleemat a shekarar 1964 a gidan mahaifinta, marigayi Ahmed Giwa, babban dan kasuwa kuma mataimakin shugaban kungiyar Jamatul Islamiyya ta kasa daga shiyyar Epe, da kuma mahaifiyarta, marigayiya Mrs. Mujibat Giwa (nee Shonibare), wata sarauniya a masarautar Kosoko, tsatson gidan Isale Eko.
Tana zaman aure da mijinta lauya, Teslim Busari (SAN).
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Wannan zai kyautata alakarmu da kai mai bibiyarmu. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don ci gaba da karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng