Tuna baya: Yadda Mahaifiya ta taba casa ni bayan ta gano ina soyayya – Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo
Mun samu labari daga Nigerian Diary cewa Farfesa Yemi Osinbajo ya bada labarin rayuwar sa a baya inda ya tabo maganar soyayyar sa a wajen wani taro da aka shirya na bangaren adabin Turanci.

Asali: Twitter
Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Farfesa Osinbajo ya bayana cewa ya fara soyayya ne tun lokacin yana ‘Dan shekara 10 a Duniya, a wancan lokacin yana Makaranta inda ya ga wata ‘Yar ajin su wanda ta burke sa kwarai da gaske.
Yemi Osinbajo yace nan-take ya rubutawa wannan Yarinya wasika dauke da wake bayan yayi kwana da kwanaki yana nazari. A wannan waken Osinbajo ya bayyanawa wannan yarinya yadda zai so su hadu da ita kafin ya bar Duniya.
KU KARANTA: Atiku Babban barawo ne na kin karawa a kasar Afrika - Rahotanni
Mataimakin Shugaban kasar ya bayyana cewa bayan ya gama tsara wannan wake kenan sai Mahaifiyar sa ta gano wasikar a cikin jakar makarantar sa, a nan ne fa Osinbajo yace aka casa shi, aka yi masa dan-karen duka a gida a ranar.
Duk da wannan dai Osinbajo ya nuna cewa bai dandara ba inda ya kinkimi wakar da ya tsara ya kai wa wannan yarinya. Bayan ya kai mata kenan, sai ya ga ta mikawa Malamin ajin su inda aka kara nemo sa aka yi masa wani danyen dukan.
Osinbajo ya bada duk wannan labari ne a wajen bikin adabi na AKE da aka saba shiryawa inda wannan karo aka yi cikin Ikeja a Jihar Legas. Bayan dukan da Osinbajo ya sha ne yace ya rabu da rubuta wakoki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng