Ba fargabar daukar ciki: Wani gawurtaccen dan luwadi ya fadi dalilin da ya sa yake neman maza

Ba fargabar daukar ciki: Wani gawurtaccen dan luwadi ya fadi dalilin da ya sa yake neman maza

Wani matashi dan shekara 23 mai suna Adamu Mohammed da ya gawurta a wajen luwadi da kananan yara a karamar hukumar Chanchaga, jihar Neja dake a Arewa ta tsakiyar Najeriya ya bayyana dalilin da yasa ya zabi yin luwadi a rayuwar sa.

Adamu wanda yanzu haka yake a hannun 'yan sandan jihar, ya shaidawa 'yan jarida cewa ya zabi zama dan luwadi ne sakamakon kasantuwar maza basu yin ciki kamar mata.

Ba fargabar daukar ciki: Wani gawurtaccen dan luwadi ya fadi dalilin da ya sa yake neman maza
Ba fargabar daukar ciki: Wani gawurtaccen dan luwadi ya fadi dalilin da ya sa yake neman maza
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Dan Al-Makura ya haye wasu mutane 6 da mota

NAIJ.com ta samu cewa 'yan sandan dai sun cafke shi ne a lokacin da yake kokarin tserewa ya bar garin bayan da wani uban yaron da yayi luwadin da shi ya kai rahoton sa wajen 'yan sandan karamar hukumar ta Chanchanga ranar Juma'ar da ta gabata.

Haka kuma dai a wani yanayi irin na tukin ganganci da izza, majiyar mu ta Tribune Online ta ruwaito mana cewa daya daga cikin 'ya'yan gwamnan jihar Nasarawa, Khalid Al-makuru ya haye akalla mutane shida da mota a daidai Mararraban Ankunza, a karamar hukumar Lafiya babban birnin jihar ta Nasarawa.

Haka nan dai kamar yadda muka samu, dagacin unguwar Ibrahim Mohammed ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace akalla ma mutum uku a cikin su sun samu munanan raunuka duk da dai cewa har yanzu ba'a samu rasa rai ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel