Ko kun san waye Bello Baba Ari - matukin jirgin da ya rasa ransa a hatsari a Abuja?

Ko kun san waye Bello Baba Ari - matukin jirgin da ya rasa ransa a hatsari a Abuja?

A jiya ne dai 'yan uwa, abokai, iyalai da ma dukkan 'yan Najeriya suka yi ta yin jimami bayan da suka samu labarin rasuwar Bello Baba-Ari, daya daga cikin matukan jiragen saman rundunar sojin Najeriya biyo bayan wani hatsari da suka yi a garin Abuja.

Sai dai ba kowa ne yasan matashin matukin jirgin ba wanda tuni har an rufe shi kamar yadda addinin muslunci ya tanada inda kuma jana'izar ta sa ta samu halartar manyan jami'an gwamnati daga sassa daban daban.

Ko kun san waye Bello Baba Ari - matukin jirgin da ya rasa ransa a hatsari a Abuja?
Ko kun san waye Bello Baba Ari - matukin jirgin da ya rasa ransa a hatsari a Abuja?
Asali: Twitter

KU KARANTA: EFCC ta soma bibiyar kudaden yan siyasa

Legit.ng ta samu cewa shi dai Marigayi Bello Baba Ari dai dan asalin jihar Yobe ne dake a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya kuma kamar yadda muka samu, shekarun sa 31 a duniya.

Haka zalika mun samu cewa Marigayin yana da aure sai dai kawo yanzu bamu tabbatar da sunan matar sa ba ko kuma suna da zuri'a a tsakani ko kuma a'a.

Da hafsan sojojin saman yake nuna juyayin sa game da marigayi, ya bayyana shi a matsayin jarumi da baya tsoron yaki kuma kwararre a wajen tukin jiragen yakin da rundunar za ta dade bata samu madadin sa ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel